Yadda aka yi sallar tsoro ranar yakin faci da tsumma(zaturruqa'a)

Musulunci > Ha > Hadith > Fihu da usulu > Yadda aka yi sallar tsoro ranar yakin faci da tsumma(zaturruqa'a)

Wanda ya ruwaito hadisin: Bukhari da Muslim suka Rawaito shi

Ingantacce ne

An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26

📖 Karatu minti 1

Rubutun hadisin: Yadda aka yi sallar tsoro ranar yakin faci da tsumma(za…

عن صالح بن خَوَّاتِ بْنِ جُبَيْرٍ رضي الله عنه عمّن صلَّى مع رسول الله صلى الله عليه وسلم صلاة ذَاتِ الرِّقَاعِ صلاةَ الخوف: أن طائفة صفَّت معه، وطائفة وِجَاهَ الْعَدُوِّ، فصلَّى بالذين معه ركعة، ثم ثبت قائما، وأتموا لأنفسهم، ثم انصرفوا، فصفُّوا وِجَاهَ الْعَدُوِّ، وجاءت الطائفة الأخرى، فصلَّى بهم الركعة التي بقيت، ثم ثبت جالسا، وأتموا لأنفسهم، ثم سلَّم بهم.

Bayanin hadisin: Yadda aka yi sallar tsoro ranar yakin faci da tsumma(za…

Annabi -tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- ya je wani yaki tare da sahabbansa yawancinsu a kasa suke,sai suka gaji har suka nannada yanki a kafafuwansu, duk da dai ba'a yi yakin ba, musulmi ne suka tsorata abokan gabarsu, to a wannan hadisin abokan gab a ba'a bangaren Alkibla suke ba,saboda gidajensu suna gabas da Madina,sai Annabi ya kasa su kashi biyu,wasu suka yi sahu tare da shi,wasu kuma suka fuskanci abokan gaba wadanda masu salla suka juya musu baya,sai Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya sallaci raka'a daya tare da sahun farko,sai suka ciko raka'a daya suka yi sallama,sannan suka je suka fuskanci abokan gaba,shi kuma ya tsaya a tsaye, har wadancan masu fuskantar abokan gaba suka zo, ya sallaci raka'ar da ta rage tare da su, sai yayi zamansa suka mike suka ciko raka'a daya,sannan yayi sallama suma suka yi.Jama'ar farko sun dace da samun kabbarar harama tare da liman,ita kuma ta biyu ta dace da samun sallama tare da liman,kuma abokan gaba basu sami dama ba,sahabbai kuma sun samu daidaito wajen samun falalar jam'in.

Rukunan : FIƘHU NA IBADA · SALLAH · FIƘHU DA USULU · SALLAR TSORO

بسم الله الرحمن الرحيم Lar 16 Jumada al-Awwal
الأربعاء 16 جمادى الأولى
أحدب متناقص Cikakken Wata Raguwa Rana 16.6 / 29.5
Haske 96%
Wata Sabo a cikin kwana 13
لا حول ولا قوة إلا بالله Babu wata ƙarfi ko iko sai na Allah

إِنَّ ٱللَّهَ وَمَلَٰٓئِكَتَهُۥ يُصَلُّونَ عَلَى ٱلنَّبِىِّ ۚ يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ صَلُّوا۟ عَلَيْهِ وَسَلِّمُوا۟ تَسْلِيمًا

Lalle, Allah da malã'ikunSa sunã salati ga Annabi. Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku yi salãti a gare shi, kuma ku yi sallama dõmin amintarwa a gare shi.

Al-Ahzab 33:56

Salati ga Manzon Allah