Lallai cewa Annabi ya aika Wani Mutum a wani yaki sai ya kasane yana" karantawa abokansa i…

Musulunci > Ha > Hadith > Alurani mai girma da ilimansa > Lallai cewa Annabi ya aika Wani Mutum a wani yaki sai ya kasane yana" karantawa abokansa i…

Wanda ya ruwaito hadisin: Bukhari da Muslim suka Rawaito shi

Ingantacce ne

An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26

📖 Karatu minti 2

Rubutun hadisin: Lallai cewa Annabi ya aika Wani Mutum a wani yaki sai y…

عن عائشة رضي الله عنها «أن رسول الله صلى الله عليه وسلم بعث رجلا على سَرِيَّةٍ فكان يَقْرَأ لأصحابه في صلاتهم، فَيَخْتِمُ بـ«قل هو الله أحد» فلما رجعوا ذكروا ذلك لرسول الله صلى الله عليه وسلم فقال: سَلُوهُ لأَيِّ شيء صَنَع ذلك؟ فسألُوه، فقال: لِأنَّها صِفَةُ الرحمن عز وجل ، فأنا أُحِب أَنْ أَقْرَأ بها، فقال رسول الله صلى الله عليه وسلم : أَخْبِرُوه: أنَّ الله تعالى يُحِبُّه».

Bayanin hadisin: Lallai cewa Annabi ya aika Wani Mutum a wani yaki sai y…

Annabi -Tsira da aminci Allah su tabbata a gareshi- ya wakilata wasu daga Sahannabnsa a kan wata Rundunar yaki, don Jagorantar ta da kuma yin hukunci a tsakaninsu, kuma don kada abin ya zama babu tsari, kuma ya zabi wanda ya fi kowanne Addini da Ilimi da kuma iya tafi da yaki, shi yasa Shugabannin sune Limamai a cikin salloli, kuma su suke bada Fatawa sabida Iliminsu da Addininsu, to sai ya rika karanta musu Kulhuwa a kowace Rakao'i biyu na kowace Sallah; sabida sonsa da Allah da kuma sunayensa da sifofinsa, kuma duk wanda yaso Allah to zai yawaita ambatonsa, to yayin da suka dawo daga yakin nasu zuwa ga Annabi sai suka gaya masa abinda ya faru sai ya cce ku tambayae shi mai yasa yake yi sai suka tambayeshi mai yasa yake yin hakan haka kawai yake yi ko kuma sabida wani abu ne? sai Jagoran nasu ya ce: ina yin haka ne Sabida ta kunshi sifofin Allah don haka nake son Maimaita ta sai Annabi ya ce ku gaya masa kamar yadda ya ke maimaita wannan sura saboda soyayyarsa da ita; kuma sabida abinda ta kunsa na sifofin Allah masu girma wanda wannan Surata kunsa na Sunayensa da aka ambata, to shima Allah yana sonsa, kai wannan ta isa falala.

Rukunan : ALƘUR'ANI MAI GIRMA DA ILIMANSA · FALALOLI NA ALƘUR'ANI · FIƘHU NA IBADA · SALLAH · ILIMIN AƘIDA · FIƘHU DA USULU · FALALOLI NA SURORI DA AYOYI · SIFFAR SALLAH · IMANI DA ALLAH MAI GIRMA DA ƊAUKAKA · Kaɗaita Allah cikin sunayenSa da siffofinSa

بسم الله الرحمن الرحيم Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
بدر Cikakken Wata Rana 16.6 / 29.5
Haske 96%
Wata Sabo a cikin kwana 13
اللهم صل على محمد Ya Allah, ka saukar da tsira a kan Muhammad

إِنَّ ٱللَّهَ وَمَلَٰٓئِكَتَهُۥ يُصَلُّونَ عَلَى ٱلنَّبِىِّ ۚ يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ صَلُّوا۟ عَلَيْهِ وَسَلِّمُوا۟ تَسْلِيمًا

Lalle, Allah da malã'ikunSa sunã salati ga Annabi. Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku yi salãti a gare shi, kuma ku yi sallama dõmin amintarwa a gare shi.

Al-Ahzab 33:56

Salati ga Manzon Allah