Manzon Allah SAW ya shafi Hannunsa a fuskarsa kuma yayi mun Addu'a , sai ya rayu shekara x…

Musulunci > Ha > Hadith > Sira da tarihi > Manzon Allah SAW ya shafi Hannunsa a fuskarsa kuma yayi mun Addu'a , sai ya rayu shekara x…

Wanda ya ruwaito hadisin: Al-Tirmithi Ya Rawaito shi - Ahmad ne ya rawaito shi

Ingantacce ne

An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26

📖 Karatu minti 1

Rubutun hadisin: Manzon Allah SAW ya shafi Hannunsa a fuskarsa kuma yayi…

عن أبي زيد بن أخْطَب رضي الله عنه قال: «مَسَح رسول الله صلى الله عليه وسلم يده على وجْهِي ودَعا لي» قال عَزْرَةُ: إنه عاش مائة وعشرين سنَة وليس في رأسه إلا شُعيْرات بِيض.

Bayanin hadisin: Manzon Allah SAW ya shafi Hannunsa a fuskarsa kuma yayi…

Manzon Allah SAW ya shafa hannunsa akan fuskar Abu zaid Bn Akhxab Al-ansari -Allah ya yarda da shi- kuma yayi Masa Addua a wata riwayar kuma ta hadisin cewa shi yayi masa Addu'a da wannan Addu'ar "Allah ka ka Qawata shi, kuma ka tabbatar da Kyawunsa" ai ka sanya shi kyakkyawa Kuma ka Sanya Kyawunsa Dawwamamme tare da shi tsawo rayuwarsa, Azara xaya daga cikin waxanda suka rawaito Hadisin yana cewa: lallai Abu Zaid Al-ansari ya rayu shekara Xari da Ashirin kuma babu Furfura akansa sa yan silalan gashi farare, kuma a cikin wata riwayar: cewa shi ya kasance ne Mai sakin Fuska kuma bashi da Mokaxar fata ko kuma nannaxewa, kuma haka ya zauna har ya Mutu, kuma wannan duk saboda Al-barkar Addu'ar Manzon Allah SAW da kuma Shafar da yayi Masa a Fuskarsa.

Rukunan : SIRAR ANNABI · ƊABI'U IRIN NA (ANNABI) MUHAMMAD · SIFFOFINSA NA HALITTA · JINƘANSA TSIRA DA AMINCIN ALLAH SU TABBATA A GARESHI · SIRA DA TARIHI · KEƁENCE-KEƁENCEN ANNABI

بسم الله الرحمن الرحيم Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
بدر Cikakken Wata Rana 16.5 / 29.5
Haske 97%
Wata Sabo a cikin kwana 13
أستغفر الله Ina neman gafara daga Allah

إِنَّ ٱللَّهَ وَمَلَٰٓئِكَتَهُۥ يُصَلُّونَ عَلَى ٱلنَّبِىِّ ۚ يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ صَلُّوا۟ عَلَيْهِ وَسَلِّمُوا۟ تَسْلِيمًا

Lalle, Allah da malã'ikunSa sunã salati ga Annabi. Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku yi salãti a gare shi, kuma ku yi sallama dõmin amintarwa a gare shi.

Al-Ahzab 33:56

Salati ga Manzon Allah