Cewa Abubakar ya shiga ga Annabi SAW bayan Wafatinsa, sai ya sanya bakinsa akan Idanunsa, …

Musulunci > Ha > Hadith > Sira da tarihi > Cewa Abubakar ya shiga ga Annabi SAW bayan Wafatinsa, sai ya sanya bakinsa akan Idanunsa, …

Wanda ya ruwaito hadisin: Ahmad ne ya rawaito shi

Hasan ne

An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26

📖 Karatu minti 1

Rubutun hadisin: Cewa Abubakar ya shiga ga Annabi SAW bayan Wafatinsa, s…

عن عائشة رضي الله عنها ، أنَّ أبا بكر دَخَل على النبي صلى الله عليه وسلم بعد وفاته، فَوَضَع فَمَهُ بَيْن عيْنَيْه، ووَضَعَ يديْه على صُدْغَيه، وقال: «وَانَبِيَّاهُ، وَاخَليلاهُ، وَاصَفِيَّاهُ».

Bayanin hadisin: Cewa Abubakar ya shiga ga Annabi SAW bayan Wafatinsa, s…

Abubakar ya shiga Wajen Manzon Allah SAW bayan Wafatinsa, sai ya sanya bakinsa a tsakanin Idanuwan Manzon ALlah SAW sai ya Sunbanceshi, kuma ya sanya Hannayensa a kan Muqamiqan Manzon ALlah SAW, su ne gefen Fuska daga Ido zuwa Kunne, kuma ya ce: "Muna rashin Annabinsa, Muna Rashin Masoyinsa, Muna rashin Zavavvensa" ai cewa shi ya kasance -Allah ya yarda da shi- yana jin ciwon Mutuwar Manzon Allah SAW kuma yana siffanta shi da cewa shi ya kasance yana fifitashi kan komai har kansa, kuma wannan shi ake kira Alhini, kuma idan bai kasance a cikinsa akwai futo na futo da Musiba da kuma raki ba, kuma idan ba'a xaga Murya ba, Kamar yadda Mata suke yi da Ihu da Kururuwa, to Wacan ya Halatta, Kuma shi ne abunda Abubakar yayi -Allah ya yarda da shi

Rukunan : SIRAR ANNABI · WAFATINSA TSIRA DA AMINCIN SU TABBATA A GARESHI · SIRA DA TARIHI

بسم الله الرحمن الرحيم Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
بدر Cikakken Wata Rana 16.5 / 29.5
Haske 97%
Wata Sabo a cikin kwana 13
اللهم صل على محمد Ya Allah, ka saukar da tsira a kan Muhammad

إِنَّ ٱللَّهَ وَمَلَٰٓئِكَتَهُۥ يُصَلُّونَ عَلَى ٱلنَّبِىِّ ۚ يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ صَلُّوا۟ عَلَيْهِ وَسَلِّمُوا۟ تَسْلِيمًا

Lalle, Allah da malã'ikunSa sunã salati ga Annabi. Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku yi salãti a gare shi, kuma ku yi sallama dõmin amintarwa a gare shi.

Al-Ahzab 33:56

Salati ga Manzon Allah