Ya ɗanɗani ɗanɗanon imani wanda ya yarda da Allah a matsayin Ubangiji, da Musulunci a mats…

Musulunci > Ha > Hadith > Ilimin aida > Ya ɗanɗani ɗanɗanon imani wanda ya yarda da Allah a matsayin Ubangiji, da Musulunci a mats…

Wanda ya ruwaito hadisin: Muslim ne ya rawaito shi

Ingantacce ne

An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26

📖 Karatu minti 2

Rubutun hadisin: Ya ɗanɗani ɗanɗanon imani wanda ya yarda da Allah a mat…

Bayanin hadisin: Ya ɗanɗani ɗanɗanon imani wanda ya yarda da Allah a mat…

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labarin cewa mumini mai gaskiya a cikin imaninsa wanda zuciyarsa ta nutsu da shi zai samu kuma zai riska a cikin zuciyarsa buɗi da yalwa da farin ciki da zaƙi, da jin daɗin kusanci ga Allah - Maɗaukakin sarki - idan ya yarda da abu uku:

Na farko: Ya yarda da Allah a matsayin Ubangiji, hakan ƙirjinsa ya buɗe ga abinda zai zo masa daga Allah da hukuncin Rububiyyah na raba arzuƙa da halaye, ba zai samu bijirewa ba a cikin zuciyarsa akan wani abu daga hakan, kuma bai nemi wani Ubangiji wanin Allah - Maɗaukakin sarki ba.

Na biyu: Ya yarda da musulunci a matsayin addini, hakan shi ne ƙirjinsa ya buɗe ga abinda musulunci ya ƙunsa na takalif da wajibai, bai tafi zuwa wanin hanyar Musulunci ba.

Na uku: Ya yarda da (Annabi) Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a matsayin Manzo, hakan shi ne ƙirjinsa ya buɗe kuma ya yi farin ciki da dukkan abinda ya zo da shi ba tare da wani kaikawo ko kokwanto ba, bai shiga (wata hanya ba) sai abinda ya dace da shiriyar Manzonsa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -.

Koyarwar hadisin: Ya ɗanɗani ɗanɗanon imani wanda ya yarda da Allah a mat…

Rukunan : ILIMIN AƘIDA · SUNAYE DA HUKUNCE-HUKUNCE · ƘARUWAR IMANI DA RAGUWARSA

بسم الله الرحمن الرحيم Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
بدر Cikakken Wata Rana 16.6 / 29.5
Haske 96%
Wata Sabo a cikin kwana 13
الله أكبر Allah Shi ne Mafi Girma

إِنَّ ٱللَّهَ وَمَلَٰٓئِكَتَهُۥ يُصَلُّونَ عَلَى ٱلنَّبِىِّ ۚ يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ صَلُّوا۟ عَلَيْهِ وَسَلِّمُوا۟ تَسْلِيمًا

Lalle, Allah da malã'ikunSa sunã salati ga Annabi. Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku yi salãti a gare shi, kuma ku yi sallama dõmin amintarwa a gare shi.

Al-Ahzab 33:56

Salati ga Manzon Allah