Lallai Allah - Mai girma da ɗaukaka - ba Ya bacci, kuma ba ya kamata gareShi Ya yi bacci

Musulunci > Ha > Hadith > Falaloli > Lallai Allah - Mai girma da ɗaukaka - ba Ya bacci, kuma ba ya kamata gareShi Ya yi bacci

Wanda ya ruwaito hadisin: Muslim ne ya rawaito shi

Ingantacce ne

An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26

📖 Karatu minti 2

Rubutun hadisin: Lallai Allah - Mai girma da ɗaukaka - ba Ya bacci, kuma…

Bayanin hadisin: Lallai Allah - Mai girma da ɗaukaka - ba Ya bacci, kuma…

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya tsaya yana mai huɗuba a cikin sahabbansa da wasu jumloli biyar cikakku, su ne: Na farko: Allah - Mai girma da ɗaukaka - ba Ya bacci. Na biyu: Bacci ya koru a cikin haƙƙinSa; saboda cikar ƘayyumiyyarSa da kuma rayuwarSa. Na uku: Allah Yana ƙasa da ma'auni kuma Yana ɗaga shi da abin da ake auna ayyukan bayin da aka ɗaukakasu masu hawa zuwa gareShi, kuma ana aunawa daga arziƙansu masu sauka zuwa ƙasa, arziƙin da shine rabon kowanne abin halitta tsarki ya tabbatar maSa Yana ƙasƙantar da shi sai Ya ƙanƙanta shi, kuma Yana ɗaukaka shi sai Ya yalwata shi. Na huɗu: Ana ɗaga abin da bayi suka aikata da daddare kafin yinin da zai zo a bayansa, da kuma aikinsu da rana kafin daren dake bayansa; Mala'iku masu kiyaye ayyuka suna hawa sama da ayyukan dare bayan ƙarewarsa a farkon yini, kuma suna hawa da ayyukan rana bayan ƙarewarsa a cikin farkon dare. Na biyar: HijabinSa mai hana ganinSa shi ne cikakken haske ko wuta, da zai yaye shi da hasken fuskarSa ya ƙona inda ganinSa ya tiƙe a halittarSa; hasken fuskarSa shi ne haskenSa da kuma ɗaukakarSa da kwarjininSa. Abin ƙaddarawa: Da a ce Ya gusar Ya yaye abin da ke hana ganinSa shine hijabi, Ya yi tajalli ga halittarSa da hasken fuskarSa sun ƙona inda ganinSa ya tiƙe daga halittarSa; sune dukkanin halittu; domin cewa ganinSa - tsarki ya tabbatar maSa Ya ɗaukaka - mai kewaye sani ne da dukkanin kasantattu.

Koyarwar hadisin: Lallai Allah - Mai girma da ɗaukaka - ba Ya bacci, kuma…

Rukunan : FALALOLI · ABUBUWA MASU TAUSASA ZUKATA DA WA'AZOZI · FALALOLIN AYYUKA NAGARI · ILIMIN AƘIDA · TUBA · FALALOLI DA LADUBBA · IMANI DA ALLAH MAI GIRMA DA ƊAUKAKA · Kaɗaita Allah cikin sunayenSa da siffofinSa

بسم الله الرحمن الرحيم Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
بدر Cikakken Wata Rana 16.5 / 29.5
Haske 97%
Wata Sabo a cikin kwana 13
سبحان الله Subhanallah - Tsarkin Allah

إِنَّ ٱللَّهَ وَمَلَٰٓئِكَتَهُۥ يُصَلُّونَ عَلَى ٱلنَّبِىِّ ۚ يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ صَلُّوا۟ عَلَيْهِ وَسَلِّمُوا۟ تَسْلِيمًا

Lalle, Allah da malã'ikunSa sunã salati ga Annabi. Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku yi salãti a gare shi, kuma ku yi sallama dõmin amintarwa a gare shi.

Al-Ahzab 33:56

Salati ga Manzon Allah