Me ya samu wasu mutane ne sun ce kaza da kaza? sai dai cewa ni ina sallah kuma ina bacci, …

Musulunci > Ha > Hadith > Sirar annabi > Me ya samu wasu mutane ne sun ce kaza da kaza? sai dai cewa ni ina sallah kuma ina bacci, …

Wanda ya ruwaito hadisin: Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi

Ingantacce ne

An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26

📖 Karatu minti 2

Rubutun hadisin: Me ya samu wasu mutane ne sun ce kaza da kaza? sai dai…

Bayanin hadisin: Me ya samu wasu mutane ne sun ce kaza da kaza? sai dai…

Wasu mutane cikin sahabbai - Allah Ya yarda da su - sun zo ɗakunan matan Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, suna tambaya game da ibadarsa a ɓoye a cikin gidansa, lokacin da aka ba su labari kamar cewa su sunga ƙanƙantarta, sai suka ce: Wane mu daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi- ? haƙiƙa an gafarta masa abinda ya gabata daga zunubinsa da abinda ya jinkirta, saɓanin wanda bai san faruwar gafara gare shi ba to yana buƙatuwa zuwa kai matuƙa a cikin ibada wataƙila ya sameta. Sannan sashinsu ya ce: Ba zan auri mata ba. Sashinsu kuma ya ce: Ba zan ci nama ba. Sashinsu kuma ya ce: Ba zan yi bacci a kan shinfiɗa ba. Sai hakan ya kai ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai ya yi fushi, ya yi wa mutane huɗuba, sai ya godewa Allah kuma ya yi yabo gare shi ya ce: Menene sha'anin wasu mutane ne sun ce kaza da kaza?! Na rantse da Allah lallai cewa nine mafi tsoronku ga Allah kuma mafi taƙawarku gare shi, sai dai cewa ni ina bacci dan in samu ƙarfi akan tsayuwar (dare), kuma ina buɗe baki dan in samu ƙarfin azimi, kuma ina auren mata, wanda ya bijire daga hanyata kuma ya ga cika a waninta, ya riƙi hanyar wanina to ba ya tare da ni.

Koyarwar hadisin: Me ya samu wasu mutane ne sun ce kaza da kaza? sai dai…

Rukunan : SIRAR ANNABI · ƊABI'U IRIN NA (ANNABI) MUHAMMAD · TSARIN ANNABI · SIRA DA TARIHI

بسم الله الرحمن الرحيم Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
بدر Cikakken Wata Rana 16.5 / 29.5
Haske 96%
Wata Sabo a cikin kwana 13
حسبنا الله ونعم الوكيل Allah Ya isa mana, Shi ne mafi kyawun Mai Kiyaye

إِنَّ ٱللَّهَ وَمَلَٰٓئِكَتَهُۥ يُصَلُّونَ عَلَى ٱلنَّبِىِّ ۚ يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ صَلُّوا۟ عَلَيْهِ وَسَلِّمُوا۟ تَسْلِيمًا

Lalle, Allah da malã'ikunSa sunã salati ga Annabi. Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku yi salãti a gare shi, kuma ku yi sallama dõmin amintarwa a gare shi.

Al-Ahzab 33:56

Salati ga Manzon Allah