Ka kasance a duniya kamar kai baƙo ne ko mai ƙetare hanya

Musulunci > Ha > Hadith > Falaloli da ladubba > Ka kasance a duniya kamar kai baƙo ne ko mai ƙetare hanya

Wanda ya ruwaito hadisin: Bukhari ne ya rawaito shi

Ingantacce ne

An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26

📖 Karatu minti 2

Rubutun hadisin: Ka kasance a duniya kamar kai baƙo ne ko mai ƙetare han…

عَنْ عَبْدِ اللَّهِ بْنِ عُمَرَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُمَا قَالَ: أَخَذَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ بِمَنْكِبِي، فَقَالَ: «كُنْ فِي الدُّنْيَا كَأَنَّكَ غَرِيبٌ أَوْ عَابِرُ سَبِيلٍ»، وَكَانَ ابْنُ عُمَرَ، يَقُولُ: إِذَا أَمْسَيْتَ فَلاَ تَنْتَظِرِ الصَّبَاحَ، وَإِذَا أَصْبَحْتَ فَلاَ تَنْتَظِرِ المَسَاءَ، وَخُذْ مِنْ صِحَّتِكَ لِمَرَضِكَ، وَمِنْ حَيَاتِكَ لِمَوْتِكَ.

Bayanin hadisin: Ka kasance a duniya kamar kai baƙo ne ko mai ƙetare han…

Ibnu Umar - Allah Ya yarda da shi - ya ambata cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya riƙe kafaɗarsa - ita ce mahaɗar damuttsa da allan kafaɗa - kuma ya ce masa:

Ka kasance a duniya kamar kai baƙo ne, wanda ya zo garin da ba shi da masauki a cikinsa da zai sauka, kuma babu wani mazaunin da zai kwantar masa da rai, ya kaɗaita daga iyalai da 'yan uwa, waɗanda sune sababin shagalta daga Mahalicci, kai ka kasance mafi tsanani daga baƙo shi ne mai ƙetare hanya mai neman ƙasarsa; domin cewa baƙo zai iya zama a garuruwan baƙunta kuma ya zauna a cikinsu, saɓanin mai ketare hanya mai nufin gari, domin cewa daga sha'aninsa saukakawa da rashin tsayuwa, da kwadayi akan saduwa da garinsa, kamar yadda matafiyi ba ya bukatuwa ga sama da abinda zai kai shi zuwa karshen tafiyarsa, haka nan mumini ba ya bukatuwa a duniya sama da abinda zai kai shi wuri.

Sai Ibnu Umar ya yi aiki da wannan nasihar kuma ya kasance yana cewa: Idan ka wayi gari to kada ka jira maraice, idan ka shiga maraice to kada ka jira safiya, ka ƙirga kanka a cikin ma'abota ƙaburbura, kuma cewa rayuwa ba ta kaɗaita daga lafiya da rashin lafiya. Ka yi gaggawa a lokutan lafiyarka da aikin ɗa'a dan rashin lafiyarka; ka ribaci ayyuka na gari a cikin lafiya kafin rashin lafiya ta tsare tsakaninka da su, ka ribaci rayuwarka a duniya, ka tara abinda zai anfaneka bayan mutuwarka.

Koyarwar hadisin: Ka kasance a duniya kamar kai baƙo ne ko mai ƙetare han…

Rukunan : ABUBUWA MASU TAUSASA ZUKATA DA WA'AZOZI · TSARKAKE ZUKATA · FALALOLI DA LADUBBA

بسم الله الرحمن الرحيم Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
بدر Cikakken Wata Rana 16.5 / 29.5
Haske 96%
Wata Sabo a cikin kwana 13
أستغفر الله Ina neman gafara daga Allah

إِنَّ ٱللَّهَ وَمَلَٰٓئِكَتَهُۥ يُصَلُّونَ عَلَى ٱلنَّبِىِّ ۚ يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ صَلُّوا۟ عَلَيْهِ وَسَلِّمُوا۟ تَسْلِيمًا

Lalle, Allah da malã'ikunSa sunã salati ga Annabi. Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku yi salãti a gare shi, kuma ku yi sallama dõmin amintarwa a gare shi.

Al-Ahzab 33:56

Salati ga Manzon Allah