Ku yi duba zuwa ga wanda yake ƙasa da ku, kada ku yi duba zuwa ga wanda yake sama da ku, h…
Musulunci > Ha > Hadith > Abubuwa masu tausasa zukata da waazozi > Ku yi duba zuwa ga wanda yake ƙasa da ku, kada ku yi duba zuwa ga wanda yake sama da ku, h…
Wanda ya ruwaito hadisin: Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Ingantacce ne
An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26
📖 Karatu minti 1
Rubutun hadisin: Ku yi duba zuwa ga wanda yake ƙasa da ku, kada ku yi du…
Bayanin hadisin: Ku yi duba zuwa ga wanda yake ƙasa da ku, kada ku yi du…
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya umarci musulmi ya yi duba a cikin al'amuran duniya a matsayi da dukiya da kuma alfarma da wasunsu zuwa ga wanda yake ƙasa da shi a hali, kuma kada ya yi duba a cikin al'amuran duniyarsa zuwa ga na sama da shi wanda ya fi shi, domin wannan duban zuwa ga na ƙasa shi ne mafi cancantar da zai sa ba zaka wulaƙanta ni'imar Allah gareka ba.
Koyarwar hadisin: Ku yi duba zuwa ga wanda yake ƙasa da ku, kada ku yi du…
- Wadatar zuci tana daga mafi girman ɗabi'un muminai, kuma ita alama ce akan yarda da ƙaddarar Allah.
- Ibnu Jarir ya ce: Wannan hadisi ne mai tattaro nau’ukan alheri; domin mutum idan ya ga wata falala a kansa a duniya sai ransa ya nemi irin hakan, kuma ya raina a binda ke gurinsa na ni'imar Allah - Maɗaukakin sarki - kuma ya yi kwaɗayin ƙari dan ya risku da hakan ko abinda ke kusa da hakan, wannan abinda ke faruwa ne a mafi yawancin mutane, amma idan ya yi duba a cikin al'amuran duniya zuwa ga wanda baikai shi ba a cikinta sai ni'imar Allah - Maɗaukakin sarki - ta bayyana agare shi, sai ya gode mata ya yi tawali'u, ya kuma aikata alheri a cikinsa.
Rukunan :
ABUBUWA MASU TAUSASA ZUKATA DA WA'AZOZI
· TSARKAKE ZUKATA
· FALALOLI DA LADUBBA
بسم الله الرحمن الرحيم
Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
سبحان الله
Subhanallah - Tsarkin Allah