Tsarki rabin imani ne , kuma (fadin) : Alhamdulillah, (wato): godiya ta tabbata ga Allah, …

Musulunci > Ha > Hadith > Ilimin aida > Tsarki rabin imani ne , kuma (fadin) : Alhamdulillah, (wato): godiya ta tabbata ga Allah, …

Wanda ya ruwaito hadisin: Muslim ne ya rawaito shi

Ingantacce ne

An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26

📖 Karatu minti 2

Rubutun hadisin: Tsarki rabin imani ne , kuma (fadin) : Alhamdulillah, (…

عن أبي مالكٍ الأشعريِّ رضي الله عنه قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم: «الطُّهُورُ شَطْرُ الْإِيمَانِ، وَالْحَمْدُ لِلهِ تَمْلَأُ الْمِيزَانَ، وَسُبْحَانَ اللهِ وَالْحَمْدُ لِلهِ تَمْلَآنِ -أَوْ تَمْلَأُ- مَا بَيْنَ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ، وَالصَّلَاةُ نُورٌ، وَالصَّدَقَةُ بُرْهَانٌ، وَالصَّبْرُ ضِيَاءٌ، وَالْقُرْآنُ حُجَّةٌ لَكَ أَوْ عَلَيْكَ، كُلُّ النَّاسِ يَغْدُو، فَبَايِعٌ نَفْسَهُ فَمُعْتِقُهَا أَوْ مُوبِقُهَا».

Bayanin hadisin: Tsarki rabin imani ne , kuma (fadin) : Alhamdulillah, (…

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labari: Cewa tsarki na zahiri yana kasancewa ne da alwala da wanka, kuma sharadi ne a sallah. Kuma cewa fadin: Alhamdulillah, (wato) "Godiya ta tabbata ga Allah yana cika ma'auni", shi ne godiya gare shi - tsarki ya tabbatar maSa - da kuma siffantaShi da siffofin cika, za'a auna su ranar alkiyama sai su cika ma'aunin ayyuka. Kuma fadin: Subhanallah, "Tsarki ya tabbata ga Allah godiya ta tabbata ga Allah", Shi ne tsarkake Shi daga kowacce tawaya da kuma siffantaShi da cikakken cika wanda yake dacewa da girmanSa, tare da sonSa da girmamaShi suna cika abinda ke tsakanin sammai da kasa. Kuma: "Sallah haske ce’’ ga bawa a cikin zuciyarsa, da fuskarsa, da cikin kabarinsa, da a tashinsa a taron Alkiyama. Kuma: "Sadaka garkuwace" kuma dalili ce akan gaskiyar imanin mumini, da kuma banbancinsa da munafikin da yake hanuwa daga yin ta (ita sadakar) dan kasancewarsa ba ya yin sadaka a lokacin ta. Kuma: "Hakuri haske ne" - Shi ne tsare rai daga firgici da fushi - wani haskene wanda yake da zafi da kuna, kamar hasken rana; domin shi mai wahalane, kuma yana bukatuwa ga dakewar zuciya da tsareta daga abinda take so; mai shi ba zai gushe ba yana mai haskaka , mai shiriya mai zarcewa akan daidai. Shi ne hakuri akan biyayya ga Allah, da kuma barin sabonSa, da kuma hakuri akan masifu da nau'o'in abubuwan ki a duniya. Kuma: 'Alkur’ani hujjane a gareka" ta hanyar Karanta shi da kuma aiki da shi, ko kuma "Hujjane akanka", ta hanyar barinsa ba tare da wani aiki ba, ko karantawa ba. Sannan - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa dukkanin mutane suna tafiya suna fita suna tashi daga barcinsu suna fita daga gidajensu dan ayyukansu mabanbanta, Daga cikinsu akwai mai tabbata akan biyayya ga Allah, sai ya 'yanto kansa daga wuta, daga cikinsu akwai wanda yake kaucewa daga hakan kuma yake afkawa a cikin sabo sai ya halakar da ita ta hanyar shigarta wuta.

Koyarwar hadisin: Tsarki rabin imani ne , kuma (fadin) : Alhamdulillah, (…

Rukunan : FIƘHU NA IBADA · TSARKI · SALLAH · FIƘHUN ADDU'O'I DA ZIKIRAI · ABUBUWA MASU TAUSASA ZUKATA DA WA'AZOZI · ILIMIN AƘIDA · FA'IDOJIN ZIKIRIN ALLAH MAI GIRMA DA ƊAUKAKA · TSARKAKE ZUKATA · FIƘHU DA USULU · ALWALA · FALALAR ALWALA · FALALAR SALLAH · FALALOLI DA LADUBBA · SUNAYE DA HUKUNCE-HUKUNCE · Yankin Imani

بسم الله الرحمن الرحيم Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
بدر Cikakken Wata Rana 16.5 / 29.5
Haske 97%
Wata Sabo a cikin kwana 13
لا إله إلا الله Babu abin bautawa sai Allah

إِنَّ ٱللَّهَ وَمَلَٰٓئِكَتَهُۥ يُصَلُّونَ عَلَى ٱلنَّبِىِّ ۚ يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ صَلُّوا۟ عَلَيْهِ وَسَلِّمُوا۟ تَسْلِيمًا

Lalle, Allah da malã'ikunSa sunã salati ga Annabi. Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku yi salãti a gare shi, kuma ku yi sallama dõmin amintarwa a gare shi.

Al-Ahzab 33:56

Salati ga Manzon Allah