(Mutum) bakwai Allah - Maɗaukakin sarki - Zai inuwantar da su a cikin inuwarSa ranar da ba…

Musulunci > Ha > Hadith > Fihu na ibada > (Mutum) bakwai Allah - Maɗaukakin sarki - Zai inuwantar da su a cikin inuwarSa ranar da ba…

Wanda ya ruwaito hadisin: Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi

Ingantacce ne

An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26

📖 Karatu minti 2

Rubutun hadisin: (Mutum) bakwai Allah - Maɗaukakin sarki - Zai inuwantar…

Bayanin hadisin: (Mutum) bakwai Allah - Maɗaukakin sarki - Zai inuwantar…

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi wa nau'i bakwai na muminai bushara cewa Allah - Maɗaukakin sarki - Zai inuwantar da su a inuwar al-ArshinSa a ranar da babu wata inuwa sai inuwarSa: Na farko: Shugaba adali a kansa ba fasiƙi ba, kuma mai adalci tsakanin talakawansa ba azzalimi ba; shi ne babban shugaba, dukkan wanda ya jiɓinci wani abu na al'amuran musulmai sai ya yi adalci a cikinsa zai risku da hakan. Na biyu: Saurayin da ya taso a cikin bautar Allah, kuma ya ƙarar da samartakarsa da nishaɗinsa, har ya mutu akan hakan. Na uku; Mutumin da zuciyarsa ta rataya da masallaci idan ya fita daga cikinsa har sai ya dawo zuwa gare shi, saboda tsananin soyayyarsa gare shi da kuma lazimtar masallacin da ci gaba da kasancewa a cikinsa da zuciya, koda wani abu mai bijirowa ya bijirowa jiki (kamar rashin lafiya) kuma ya zama a wajen masallacin. Na huɗu; Mutum biyu kowane ɗaya daga cikinsu ya so ɗayan saboda Allah a haƙiƙa, kuma suka dawwama akan soyayyar Addini wani abu mai bijirowa na duniya bai rabasu ba daidai ne sun haɗu a haƙiƙa ko a'a har mutuwa ta rabasu. Na biyar: Da mutumin da mace ta neme shi akan kanta dan aikata alfasha, kuma mai asali ce da ɗaukaka da matsayi da alfarma da dukiya da kyau, sai ya ƙi kuma ya ce: Ni ina jin tsoron Allah. Na shida: Mutumin da ya yi sadaka kaɗan ce ko mai yawa bai yi riya a cikinta ba kai ya ɓoyeta har hagunsa bata sanin abinda damansa take ciyarwa. Na bakwai: Mutumin da ya ambaci Allah da zuciyarsa daga tinani ne, ko da harshensa na zikiri, a keɓance daga mutane sai hawaye suka kwaranyo daga idanuwansa dan jin tsoron Allah da kuma girmama Shi - Maɗaukakin sarki -.

Koyarwar hadisin: (Mutum) bakwai Allah - Maɗaukakin sarki - Zai inuwantar…

Rukunan : FIƘHU NA IBADA · SALLAH · FIƘHUN ADDU'O'I DA ZIKIRAI · ABUBUWA MASU TAUSASA ZUKATA DA WA'AZOZI · FA'IDOJIN ZIKIRIN ALLAH MAI GIRMA DA ƊAUKAKA · TSARKAKE ZUKATA · FIƘHU DA USULU · FALALOLI DA LADUBBA · HUKUNCE-HUKUNCEN MASALLATAI

بسم الله الرحمن الرحيم Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
بدر Cikakken Wata Rana 16.6 / 29.5
Haske 96%
Wata Sabo a cikin kwana 13
سبحان الله Subhanallah - Tsarkin Allah

إِنَّ ٱللَّهَ وَمَلَٰٓئِكَتَهُۥ يُصَلُّونَ عَلَى ٱلنَّبِىِّ ۚ يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ صَلُّوا۟ عَلَيْهِ وَسَلِّمُوا۟ تَسْلِيمًا

Lalle, Allah da malã'ikunSa sunã salati ga Annabi. Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku yi salãti a gare shi, kuma ku yi sallama dõmin amintarwa a gare shi.

Al-Ahzab 33:56

Salati ga Manzon Allah