Lallai ni ina jiye muku tsoro a baya na, abinda za'a buɗe muku na ƙawar duniya da adonta

Musulunci > Ha > Hadith > Abubuwa masu tausasa zukata da waazozi > Lallai ni ina jiye muku tsoro a baya na, abinda za'a buɗe muku na ƙawar duniya da adonta

Wanda ya ruwaito hadisin: Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi

Ingantacce ne

An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26

📖 Karatu minti 3

Rubutun hadisin: Lallai ni ina jiye muku tsoro a baya na, abinda za'a bu…

Bayanin hadisin: Lallai ni ina jiye muku tsoro a baya na, abinda za'a bu…

Wata rana Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya zauna akan minbari yana karantar da sahabbansa sai ya ce:

Lallai cewa mafi yawancin abinda nake jiye muku tsoro a bayana (shi ne) abinda za'a buɗa muku na albarkatun ƙasa da ƙawace-ƙawacen duniya da adonta da kyanta, da abinda ke cikinta na nau'ikan jin daɗi da tufa da shukoki da wasunsu daga abinda mutane suke alfahari da kyawunsu tare da ƙarancin wanzuwa.

Sai wani mutum ya ce: Kawace-ƙawacen duniya ni'imace daga Allah, shin wannan ni'imar zata dawo ta zama azaba da uƙuba?!

Sai mutane suka zargi mai tambayar yayin da suka gan shi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi shiru, suka zaci cewa ya fusatar da shi ne.

Sai ya bayyana cewa shi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance wahayi yana saukar masa ne, sannan ya fara shafe gumi daga goshinsa, sai ya ce: Ina mai tambaya?

Ya ce: Ni ne.

Sai ya godewa Allah ya yi yabo a gareShi, sannan tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: Alheri na haƙiƙa ba ya zuwa da (komai) sai da alheri, sai dai waɗannan ƙawace-ƙawacen ba tsantsar alheri bane saboda abinda suke kaiwa gare shi na fitina da gasa da shagaltuwa da su daga cikar fuskantar lahira, sai ya buga misali ga hakan sai ya ce:

Lallai tsiron kaka da korensa, shi wani nau'i ne na shuka da yake ƙayatar da dabbobi sai ya yi kisa dan yawan ci da cikaciki ko ya kusa yin kisa, sai (dabba) mai cin koriyar ciyawa ta ci har ta cika kwiɓinan cikinta, sai ta fuskanci rana ta yi toroso daga cikinta a sirance ko ta yi fitsari, sannan ta nemi daga abinda ke cikin hantarta sai ta tauna shi sannan ta hadiye shi, sannan ta dawo sai ta cinye.

Domin cewa wannan dukiyar kamar maɓungura ƙasane koraye mai zaƙi, yana kisa ko yana kusa ya yi kisa saboda yawansa; sai dai idan ya taƙaita daga gare shi akan kaɗan ɗin da buƙatuwa take isa zuwa gareshi, kuma isuwa take samuwa da shi ta hanyar halal domin cewa shi ba ya cutarwa, madalla dana musulmi wanda shi ga wanda ya ba wa miskini da maraya da matafiyi daga gareta, wanda ya karɓeta da haƙƙinta za’a yi masa albarka a cikinta, wanda ya karɓeta ba tare da haƙƙinta ba to kwatankwacinsa kamar kwatankwacin wanda yake ci ne ba ya ƙoshi, kuma zata zama mai shaida akansa a ranar alƙiyama.

Koyarwar hadisin: Lallai ni ina jiye muku tsoro a baya na, abinda za'a bu…

Rukunan : ABUBUWA MASU TAUSASA ZUKATA DA WA'AZOZI · ZARGIN SON DUNIYA · FALALOLI DA LADUBBA

بسم الله الرحمن الرحيم Lar 16 Jumada al-Awwal
الأربعاء 16 جمادى الأولى
أحدب متناقص Cikakken Wata Raguwa Rana 16.7 / 29.5
Haske 96%
Wata Sabo a cikin kwana 13
سبحان الله Subhanallah - Tsarkin Allah

إِنَّ ٱللَّهَ وَمَلَٰٓئِكَتَهُۥ يُصَلُّونَ عَلَى ٱلنَّبِىِّ ۚ يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ صَلُّوا۟ عَلَيْهِ وَسَلِّمُوا۟ تَسْلِيمًا

Lalle, Allah da malã'ikunSa sunã salati ga Annabi. Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku yi salãti a gare shi, kuma ku yi sallama dõmin amintarwa a gare shi.

Al-Ahzab 33:56

Salati ga Manzon Allah