Iyalan (Annabi) Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ba su taɓa cin ab…
Musulunci > Ha > Hadith > Abubuwa masu tausasa zukata da waazozi > Iyalan (Annabi) Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ba su taɓa cin ab…
Wanda ya ruwaito hadisin: Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Ingantacce ne
An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26
📖 Karatu minti 1
Rubutun hadisin: Iyalan (Annabi) Muhammad - tsira da amincin Allah su ta…
Bayanin hadisin: Iyalan (Annabi) Muhammad - tsira da amincin Allah su ta…
Uwar muminai Nana A'isha - Allah Ya yarda da ita - tana bada labarin cewa iyalan gidan Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - basu taɓa cin abinci sau biyu ba a rana ɗaya sai ɗayan ya zama dabino ne.
Koyarwar hadisin: Iyalan (Annabi) Muhammad - tsira da amincin Allah su ta…
- Tawali'un Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da iyalan gidansa, sauda yawa a rana ɗaya ma basu samun wani abin da zasu ci sai abinci ɗaya.
- Dabino ya kasance shine mafi sauƙi a wurinsu akan waninsa.
- Falalar gudun duniya da wadatuwa da kaɗan a rayuwa, kuma kasancewarsa yana daga ɗabi'un Annabawa, da kuma tarihin shugaban Manzanni.
- Cin abinci sau biyu a rana ɗaya yana daga cikin al'amuran da aka halatta, kuma hakan yana daga cikin sanannun al'adun larabawa, domin sun kasance a rana ɗaya suna ci ne sau biyu, abincin rana da abincin dare.
Rukunan :
ABUBUWA MASU TAUSASA ZUKATA DA WA'AZOZI
· ZUHUDU DA TSANTSENI
· SIRAR ANNABI
· ƊABI'U IRIN NA (ANNABI) MUHAMMAD
· FALALOLI DA LADUBBA
· TSARIN ANNABI
· SIRA DA TARIHI
بسم الله الرحمن الرحيم
Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
لا إله إلا الله
Babu abin bautawa sai Allah