Kara Surah Ad-Duha

Surah Ad-Duha (الضحى) ita ce surah na Makka ta Alkur'ani tana da ayoyi 11. Ku karanta, ku saurari kuma ku hadda wannan surah tare da kayanmu masu hulɗa.

An sabunta a 05 Agusta 2026 16h34

📖 Karatu minti 1

Surah Ad-Duha cikin lambobi

Tsarin saukarwa
Saukarwa n° 11 / 114
(na Makka)
40
kalmomi
-94.4% vs matsakaici
170
haruffa
-94.5% vs matsakaici
1
min karantawa
11
ayoyi
-79.9% vs matsakaici

Yawan amfani da kalmomin bincike

الله 0
رب 3

Haruffa da yawa suke fitowa

ل
18
#1
ا
16
#2
و
15
#3
م
10
#4
ي
9
#5
الضحى · Juz 30
Kara Surah Ad-Duha
سورة الليل
Juz 30 72.2% (407/564)
Hizb 60 45.5% (131/288)

وَٱلضُّحَىٰ ﴿١﴾

Inã rantsuwa da hantsi.

وَٱلَّيْلِ إِذَا سَجَىٰ ﴿٢﴾

Da dare a lõkacin da ya rufe (da duhunsa).

مَا وَدَّعَكَ رَبُّكَ وَمَا قَلَىٰ ﴿٣﴾

Ubangijinka bai yi maka bankwana ba, kuma bai ƙĩ kaba.

وَلَلْـَٔاخِرَةُ خَيْرٌۭ لَّكَ مِنَ ٱلْأُولَىٰ ﴿٤﴾

Kuma lalle ta ƙarshe ce mafi alheri a gare ka daga ta farko.

وَلَسَوْفَ يُعْطِيكَ رَبُّكَ فَتَرْضَىٰٓ ﴿٥﴾

Kuma lalle ne, Ubangijinka zai yi ta bã ka kyauta sai ka yarda.

أَلَمْ يَجِدْكَ يَتِيمًۭا فَـَٔاوَىٰ ﴿٦﴾

Ashe, bai sãme ka marãya ba, sa'an nan Ya yi maka makõma?

وَوَجَدَكَ ضَآلًّۭا فَهَدَىٰ ﴿٧﴾

Kuma Ya sãme ka bã ka da shari'ã, sai Ya shiryar da kai?

وَوَجَدَكَ عَآئِلًۭا فَأَغْنَىٰ ﴿٨﴾

Kuma Ya sãme ka matalauci, sai Ya wadãtã ka?

فَأَمَّا ٱلْيَتِيمَ فَلَا تَقْهَرْ ﴿٩﴾

Sabõda haka, amma marãya, to, kada ka rinjãye shi.

وَأَمَّا ٱلسَّآئِلَ فَلَا تَنْهَرْ ﴿١٠﴾

Kuma amma mai tambaya, kada ka yi masa tsãwa.

وَأَمَّا بِنِعْمَةِ رَبِّكَ فَحَدِّثْ ﴿١١﴾

Kuma amma ni'imar Ubangijinka, sai ka faɗa (dõmin gõdiya).

بسم الله الرحمن الرحيم Lit 10 Rabi' al-Awwal
الاثنين 10 ربيع الأول
أحدب متزايد Cikakken Wata Tasowa Rana 11.5 / 29.5
Haske 89%
Cikakken Wata a cikin kwana 3
لا حول ولا قوة إلا بالله Babu wata ƙarfi ko iko sai na Allah