Idan kaga wadanda suke bin masu kama da juna daga gareshi to wadannan su ne Allah Ya ambat…

Musulunci > Ha > Hadith > Alurani mai girma da ilimansa > Idan kaga wadanda suke bin masu kama da juna daga gareshi to wadannan su ne Allah Ya ambat…

Wanda ya ruwaito hadisin: Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi

Ingantacce ne

An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26

📖 Karatu minti 2

Rubutun hadisin: Idan kaga wadanda suke bin masu kama da juna daga gares…

عَنْ ‌عَائِشَةَ رَضِيَ اللهُ عَنْهَا قَالَتْ: تَلَا رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ هَذِهِ الْآيَةَ: {هُوَ الَّذِي أَنْزَلَ عَلَيْكَ الْكِتَابَ مِنْهُ آيَاتٌ مُحْكَمَاتٌ هُنَّ أُمُّ الْكِتَابِ وَأُخَرُ مُتَشَابِهَاتٌ فَأَمَّا الَّذِينَ فِي قُلُوبِهِمْ زَيْغٌ فَيَتَّبِعُونَ مَا تَشَابَهَ مِنْهُ ابْتِغَاءَ الْفِتْنَةِ وَابْتِغَاءَ تَأْوِيلِهِ، وَمَا يَعْلَمُ تَأْوِيلَهُ إِلَّا اللَّهُ، وَالرَّاسِخُونَ فِي الْعِلْمِ يَقُولُونَ آمَنَّا بِهِ كُلٌّ مِنْ عِنْدِ رَبِّنَا وَمَا يَذَّكَّرُ إِلَّا أُولُو الْأَلْبَابِ} [آل عمران: 7]. قَالَتْ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «فَإِذَا رَأَيْتِ الَّذِينَ يَتَّبِعُونَ مَا تَشَابَهَ مِنْهُ فَأُولَئِكَ الَّذِينَ سَمَّى اللهُ، فَاحْذَرُوهُمْ».

Bayanin hadisin: Idan kaga wadanda suke bin masu kama da juna daga gares…

Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya karanta wannan ayar:{Shi ne wanda ya saukar maka da littafi daga cikinsa akwai ayoyi bayyanannu su ne mafi yawan littafi da wasu masu kama da juna, amma wadanda a cikin zukatansu akwai karkata sai suke bin abinda ya yi kama da juna daga gare shi dan neman fitina da neman tawilinsa, kuma babu wanda ya san tawilinsa sai Allah, matabbata a cikin ilimi suna cewa mun yi imani da shi dukkansa daga gurin Ubangijinmu ne Ba mai tunani sai ma'abota hankalu}.

a cikin wannan ayar Allah - tsarki ya tabbatar maSa -Ya bada labari cewa Shi ne wanda Ya saukar da Alkur’ani ga AnnabinSa, wanda daga cikinsa akwai wasu ayoyi masu bayyananar nuni, hukunce-hukuncensu sanannu ne babu rikici a cikinsu, su ne asalin littafi kuma makomarsa, su ne makoma yayin sabani, daga cikinsa akwai wasu ayoyin daban masu daukar sama da ma'ana, ma'anarsu tana rikitarwa ga wasu daga mutane, ko ya zaci cewa tsakakninsu da wata ayar akwai karo, sannan Allah Ya bayyana mu'amalar mutane tare da wadannan ayoyin.

wadanda a cikin zukatansu akwai karkata daga gaskiya sai su bar bayyayanannu, su yi riko da masu kama da juna masu daukar ma'anoni sama da daya, suna neman tayar da rikici ta hakan da batar da mutane, kuma suna neman tawilinsu akan abinda ya dace da son ransu, amma matabbata a cikin ilimi to cewa su suna sanin wadannan masu kama da junan, suna dawo da shi ga bayyananne, kuma suna yin imani da shi kuma cewa shi daga gurin Allah yake - Madaukakin sarki -, ba zai yiwu ya rikitar ba ko ya yi karo da juna, saidai ba mai tunanin hakan sai mai wa'azantuwa ma'abota hankula lafiyayyu.

Sannan Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce wa Uwar Muminai A'isha - Allah Ya yarda da ita - cewa ita idan ta ga wadanda suke neman masu kama da juna to cewa su ne wadanda Allah Ya ambace su a cikin fadinSa; {Amma wadanda a cikin zukatansu akwai karkata} to ku gujesu kada ku karkata zuwa gare su.

Koyarwar hadisin: Idan kaga wadanda suke bin masu kama da juna daga gares…

Rukunan : ALƘUR'ANI MAI GIRMA DA ILIMANSA · TAFSIRIN ALƘUR'ANI · ABUBUWA MASU TAUSASA ZUKATA DA WA'AZOZI · CUTUTTUKAN ZUKATA · ZARGIN SON ZUCIYA DA SHA'AWE-SHA'AWE · FALALOLI DA LADUBBA · TAFSIRIN AYOYI

بسم الله الرحمن الرحيم Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
بدر Cikakken Wata Rana 16.6 / 29.5
Haske 96%
Wata Sabo a cikin kwana 13
أستغفر الله Ina neman gafara daga Allah

إِنَّ ٱللَّهَ وَمَلَٰٓئِكَتَهُۥ يُصَلُّونَ عَلَى ٱلنَّبِىِّ ۚ يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ صَلُّوا۟ عَلَيْهِ وَسَلِّمُوا۟ تَسْلِيمًا

Lalle, Allah da malã'ikunSa sunã salati ga Annabi. Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku yi salãti a gare shi, kuma ku yi sallama dõmin amintarwa a gare shi.

Al-Ahzab 33:56

Salati ga Manzon Allah