Musulunci > Ha > Hadith > Ilimin aida > Ni ne Dimam dan Sa'alabata dan uwan Banu Sa'ad dan Bakar
Ingantacce neAn sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26
📖 Karatu minti 2عن أَنَسَ بْنَ مَالِكٍ رضي الله عنه قال: بينما نحن جلوس مع النبي صلى الله عليه وسلم في المسجد دخل رجل على جمل، فأناخه في المسجد ثم عقله، ثم قال لهم: أيكم محمد؟ والنبي صلى الله عليه وسلم متكئ بين ظهرانيهم، فقلنا: هذا الرجل الأبيض المتكئ. فقال له الرجل: يا ابن عبد المطلب فقال له النبي صلى الله عليه وسلم: «قد أجبتك». فقال الرجل للنبي صلى الله عليه وسلم: إني سائلك فمشدد عليك في المسألة، فلا تجد علي في نفسك؟ فقال: «سل عما بدا لك» فقال: أسألك بربك ورب من قبلك، آلله أرسلك إلى الناس كلهم؟ فقال: «اللهم نعم». قال: أنشدك بالله، آلله أمرك أن نصلي الصلوات الخمس في اليوم والليلة؟ قال: «اللهم نعم». قال: أنشدك بالله، آلله أمرك أن نصوم هذا الشهر من السنة؟ قال: «اللهم نعم». قال: أنشدك بالله، آلله أمرك أن تأخذ هذه الصدقة من أغنيائنا فتقسمها على فقرائنا؟ فقال النبي صلى الله عليه وسلم: «اللهم نعم». فقال الرجل: آمنت بما جئت به، وأنا رسول من ورائي من قومي، وأنا ضمام بن ثعلبة أخو بني سعد بن بكر.
Anas dan Malik - Allah Ya yarda da shi - yana bada labarin cewa: Lokacin da sahabbai suna zaune tare da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a cikin masallaci yayin da wani mutum ya shigo akan wani rakumi, sai ya durkusar da rakumin sannan ya daure shi. Sannan ya tambayesu: Waye Muhammd a cikinku? Alhali Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana kishingide tsakanin mutanen, sai muka ce : Wannan farin mutumin. Sai mutumin ya ce da shi: Yakai Dan Abdul Muddalib. Sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce da shi: Na ji ka yi tambaya in amsa maka. Sai mutumin ya cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: Ni mai tambayarka ne kuma mai tsananta maka a tambaya, kada ka ji wani abu game dani a ranka. Wato: Kada ka yi fushi da ni kuma kada kunci ya sameka. Sai ya ce: Ka tambayi abinda kake so. Sai ya ce: Ina ina hada ka da Ubangijinka kuma Ubangijin wadanda suka gabace ka, shin Allah ne Ya aikoka zuwa ga mutane? Sai ya ce: Eh ya Allah, dan karfafa gaskiyarsa. Sai Mutumin ya ce: Ina yi maka magiya da Allah, wato; Ina tambayarka sabo da Allah, shin Allah ne Ya umarceka da ka yi salloli biyar a yini da dare? Su ne salloli wadanda aka faralanta ?., Ya ce: Eh ya Allah, Ya ce: Ina maka magiya da Allah, shin Allah ne Ya umarceka da mu azimci wannan watan daga shekara? wato: Watan Ramadan, Ya ce: Eh ya Allah, Ya ce: Ina maka magiya da Allah, shin Allah ne Ya umarceka daka karbi wannan sadakar daga mawadatanmu sai ka rabata ga talakawanmu? ita ce zakka. Sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: Eh ya Allah, Sai Dimam ya musulunta, kuma ya ba Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - labarin cewa shi zai kira mutanensa zuwa Musulunci. Sannan ya yi bayanin kansa cewa shi ne Dimam dan Sa'alabata daga Banu Sa'ad Ibnu Bakar.
Rukunan : FIƘHU NA IBADA · SALLAH · ZAKKA · AZUMI · ILIMIN AƘIDA · DA'AWA ZUWA GA ALLAH · FIƘHU DA USULU · WAJIBCIN SALLAH DA HUKUNCIN MAI BARINTA · WAJIBCIN ZAKKKA DA HUKUNCIN MAI ƘIN BAYARWA · Obligation of Fasting and Ruling of Its Abandoning · IMANI DA ALLAH MAI GIRMA DA ƊAUKAKA · DA'AWA DA HISBA · Imani da Manzanni · SUNAYE DA HUKUNCE-HUKUNCE · ANNABIMMU MUHAMMAD TSIRA DA AMINCIN ALLAH SU TABBATA A GARESHI · MUSULUNCI