Dinaren da ka ciyar da shi a cikin tafarkin Allah, da dinaren da ka ciyar da shi a 'yanta …
Musulunci > Ha > Hadith > Fihu na ibada > Dinaren da ka ciyar da shi a cikin tafarkin Allah, da dinaren da ka ciyar da shi a 'yanta …
Wanda ya ruwaito hadisin: Muslim ne ya rawaito shi
Ingantacce ne
An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26
📖 Karatu minti 1
Rubutun hadisin: Dinaren da ka ciyar da shi a cikin tafarkin Allah, da d…
Bayanin hadisin: Dinaren da ka ciyar da shi a cikin tafarkin Allah, da d…
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ambaci sashin nau’ukan ciyarwa, sai ya ce: Dinarin da ka ciyar da shi a yaƙi a tafarkin Allah, da dinarin da ka ciyar da shi a 'yanta wuyaye da bauta, da dinarin da ka yi sadaka ga miskini mabuƙaci, da dinarin da ka ciyar da shi ga iyalanka, sannan ya bada labarin cewa mafi girmansu a lada a wajen Allah shi ne wanda ka ciyar da shi ga iyalanka da wanda ciyar da shi ya lazimceka.
Koyarwar hadisin: Dinaren da ka ciyar da shi a cikin tafarkin Allah, da d…
- Yawan ƙofofin ciyarwa a tafarkin Allah.
- Gabatar da abin da ya fi a cikin babin ciyarwa a lokacin cinkoso, yana daga hakan ciyarwa ga iyali a lokacin da ciyarwa ga gabaɗayan ba zai yi wu ba.
- Nawawi ya faɗa a Sharhin Muslim: Kwaɗaitarwa akan ciyarwa ga iyalai, da kuma bayanin girman lada a cikinta; domin daga cikinsu akwai wanda ciyarwarsa take wajaba ta hanyar kusanci, daga cikinsu akwai wanda take zama mustahabbi kuma tana zama sadaka da sada zumunci, kuma daga cikinsu akwai wadda take zama wajiba ta hanyar mallakar aure ko mallakar dama (bayi), wannan dukkansa mai falala ne kuma abin kwaɗaitarwa ne a kansa, kuma shi ya fi sadakar nafila.
- Sindi ya ce: Faɗinsa: (Dinaren da yake ciyar da shi ga iyalansa), wato: Idan ya yi hakan don Allah kuma ya yi nufin haƙƙin iyalai misali.
- Abu Kilaba ya ce; Wane mutum ne mafi girman lada daga mutumin da yake ciyarwa ga iyalai ƙanana da zai karesu ko Allah Ya anfanar da su da shi kuma ya wadata su?!
Rukunan :
FIƘHU NA IBADA
· FIƘHU NA ZAMANTAKEWAR IYALI
· ZAKKA
· CIYARWA
· FIƘHU DA USULU
· SADAKA TA NAFILA
بسم الله الرحمن الرحيم
Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
لا حول ولا قوة إلا بالله
Babu wata ƙarfi ko iko sai na Allah