Ya kai baffana, ka ce : Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kalma ce wacce zan kafa ma…

Musulunci > Ha > Hadith > Alurani mai girma da ilimansa > Ya kai baffana, ka ce : Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kalma ce wacce zan kafa ma…

Wanda ya ruwaito hadisin: Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi

Ingantacce ne

An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26

📖 Karatu minti 2

Rubutun hadisin: Ya kai baffana, ka ce : Babu abin bautawa da gaskiya sa…

عن سَعِيدِ بْنِ الْمُسَيَّبِ، عَنْ أَبِيهِ قَالَ: لَمَّا حَضَرَتْ أَبَا طَالِبٍ الْوَفَاةُ، جَاءَهُ رَسُولُ اللهِ صلى الله عليه وسلم فَوَجَدَ عِنْدَهُ أَبَا جَهْلٍ وَعَبْدَ اللهِ بْنَ أَبِي أُمَيَّةَ بْنِ الْمُغِيرَةِ، فَقَالَ: «أَيْ عَمِّ، قُلْ: لَا إِلَهَ إِلَّا اللهُ، كَلِمَةً أُحَاجُّ لَكَ بِهَا عِنْدَ اللهِ»، فَقَالَ أَبُو جَهْلٍ وَعَبْدُ اللهِ بْنُ أَبِي أُمَيَّةَ: أَتَرْغَبُ عَنْ مِلَّةِ عَبْدِ الْمُطَّلِبِ، فَلَمْ يَزَلْ رَسُولُ اللهِ صلى الله عليه وسلم يَعْرِضُهَا عَلَيْهِ، وَيُعِيدَانِهِ بِتِلْكَ الْمَقَالَةِ، حَتَّى قَالَ أَبُو طَالِبٍ آخِرَ مَا كَلَّمَهُمْ: عَلَى مِلَّةِ عَبْدِ الْمُطَّلِبِ، وَأَبَى أَنْ يَقُولَ: لَا إِلَهَ إِلَّا اللهُ، قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صلى الله عليه وسلم: «وَاللهِ لَأَسْتَغْفِرَنَّ لَكَ مَا لَمْ أُنْهَ عَنْكَ»، فَأَنْزَلَ اللهُ: {مَا كَانَ لِلنَّبِيِّ وَالَّذِينَ آمَنُوا أَنْ يَسْتَغْفِرُوا لِلْمُشْرِكِينَ} [التوبة: 113]، وَأَنْزَلَ اللهُ فِي أَبِي طَالِبٍ، فَقَالَ لِرَسُولِ اللهِ صلى الله عليه وسلم: {إِنَّكَ لا تَهْدِي مَنْ أَحْبَبْتَ وَلَكِنَّ اللهَ يَهْدِي مَنْ يَشَاءُ} [القصص: 56].

Bayanin hadisin: Ya kai baffana, ka ce : Babu abin bautawa da gaskiya sa…

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya shiga wurin baffansa Abu Dalib alhali shi yana kan gargara, sai ya ce masa: Ya baffana, ka ce : "Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, wata kalmace da zan yi maka shaida da ita a wurin Allah, sai Abu Jahal da Abdullahi Dan Abu Umayya suka ce: Ya Abu Dalib, zaka bar tafarkin babanka Abdul Muddalib?! Shi ne bautar gumaka, basu gushe ba suna yi masa magana har ya fadi karshen wani abinda ya zantar da su da shi: Akan tafarkin Abdul Muddalib, tafarkin shirka da bautar gumaka, sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: Zan roka maka gafara muddin Ubangijina bai hanani hakan ba, sai fadin Allah - Madaukakin sarki - ya sauka: {Bã ya kasancẽwa ga Annabi da waɗanda suka yi ĩmãni, su yi istigifãri ga mushirikai, kuma kõ dã sun kasance ma'abũta zumunta ne daga bãyan sun bayyana a gare su, cẽwa lalle ne, sũ, 'yan Jahĩm ne} [Al-Taubah: 113], kuma fadin Allah - Madaukakin sarki - ya sauka a sha'anin Abu Dalib: {Lalle ne kai bã ka shiryar da wanda ka so, amma kuma Allah Yanã shiryar da wanda Yake so, kuma Shi ne Mafi sani daga mãsu shiryuwa} [Al-kasas: 56], lallai cewa kai ba ka shiryar da wanda ka so shiriyarsa, kawai kai isarwa ce taka, Allah Yana shiryar da wanda yake so.

Koyarwar hadisin: Ya kai baffana, ka ce : Babu abin bautawa da gaskiya sa…

Rukunan : ALƘUR'ANI MAI GIRMA DA ILIMANSA · TAFSIRIN ALƘUR'ANI · DA'AWA ZUWA GA ALLAH · DA'AWA DA HISBA

بسم الله الرحمن الرحيم Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
بدر Cikakken Wata Rana 16.5 / 29.5
Haske 97%
Wata Sabo a cikin kwana 13
الحمد لله Alhamdulillah - Godiya ta tabbata ga Allah

إِنَّ ٱللَّهَ وَمَلَٰٓئِكَتَهُۥ يُصَلُّونَ عَلَى ٱلنَّبِىِّ ۚ يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ صَلُّوا۟ عَلَيْهِ وَسَلِّمُوا۟ تَسْلِيمًا

Lalle, Allah da malã'ikunSa sunã salati ga Annabi. Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku yi salãti a gare shi, kuma ku yi sallama dõmin amintarwa a gare shi.

Al-Ahzab 33:56

Salati ga Manzon Allah