Musulunci > Ha > Hadith > Ilimin aida > Lallai ni ina barranta zuwa ga Allah da ya zama ina da badadi daga cikinku, to lallai cewa…
Ingantacce neAn sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26
📖 Karatu minti 1عن جندب رضي الله عنه قال: سَمِعْتُ النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَبْلَ أَنْ يَمُوتَ بِخَمْسٍ وَهُوَ يَقُولُ «إِنِّي أَبْرَأُ إِلَى اللهِ أَنْ يَكُونَ لِي مِنْكُمْ خَلِيلٌ فَإِنَّ اللهَ تَعَالَى قَدِ اتَّخَذَنِي خَلِيلًا كَمَا اتَّخَذَ إِبْرَاهِيمَ خَلِيلًا، وَلَوْ كُنْتُ مُتَّخِذًا مِنْ أُمَّتِي خَلِيلًا لَاتَّخَذْتُ أَبَا بَكْرٍ خَلِيلًا! أَلَا وَإِنَّ مَنْ كَانَ قَبْلَكُمْ كَانُوا يَتَّخِذُونَ قُبُورَ أَنْبِيَائِهِمْ وَصَالِحِيهِمْ مَسَاجِدَ، أَلَا فَلَا تَتَّخِذُوا الْقُبُورَ مَسَاجِدَ! إِنِّي أَنْهَاكُمْ عَنْ ذَلِكَ».
Annabi - tsira da amincinAllah su tabbata a gare shi - ya sanar game da darajarsa a wurin Allah - Madaukain sarki -, kuma cewa ita takai mafi kololuwar darajojin soyayya, kamar yadda (Annabi ) Ibrahim - amincin Allah ya tabbata a gare shi - ya sameta, saboda haka ne ya kore ya zama cewa yana da wani badadi wanin Allah; domin cewa zuciyarsa ta cika da soyayyar Allah - Madaukakin sarki - da girmama Shi da saninsa, to ba ta yalwatuwa ga wani koma bayan Allah. Da a ce yana da wani badadi daga halitta da ya zama sayyidin Abubakar - Allah Ya yarda da shi -. Sannan ya yi gargadi daga ketare iyakar da ta halatta a cikin soyayya kamar yadda Yahudawa da Nasara suka aikata a kaburburan Annabawansu da salihansu har suka maida su alloli na shirka ana bauta musu koma bayan Allah, kuma suka sanya siminti da kayan alatu a kaburburan dake masallatai da guraren ibada, kuma tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya hana al'ummarsa da su aikata irin aikinsu.
Rukunan : FALALAR SAHABBAI · ILIMIN AƘIDA · IMANI DA ALLAH MAI GIRMA DA ƊAUKAKA · SAHABBAI · Kaɗaita Allah cikin bauta