Musulunci > Ha > Hadith > Falaloli da ladubba > Manzon Allah ya hana sanya alhariri sai a gurin yatsu biyu, ko uku, ko hudu.
Ingantacce neAn sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26
📖 Karatu minti 1عن عمر بن الخطاب رضي الله عنه أَنَّ رَسُولَ الله صلى الله عليه وسلم «نهى عن لُبُوسِ الحَرِيرِ إلا هكذا، ورَفَعَ لنا رسول الله صلى الله عليه وسلم أُصْبُعَيْهِ: السَّبَّابَةَ، والوُسْطَى».
ولمسلم «نهى رسول الله صلى الله عليه وسلم عن لُبْس ِالحَرِيرِ إلا مَوْضِعَ أُصْبُعَيْنِ، أو ثلاثٍ، أو أربعٍ».
Lallai Manzon Allah tsira da amincin Allah ya hana maza sanya alhariri sai dai a inda aka kebance, watau y'an yatsu biyu da aka ambata cikin hadisin Buhari da Muslim da ya gabata da kuma ruwayar Muslim da ta kara da cewa: ko uku ko hudu, don haka sai a yi amfani da mafi yawa, shi ne gwargwadon yatsu hudu ba laifi. ka duba Littafin Taasisil'Ahkam
Rukunan : LADUBBA NA SHARI'A · LADUBBAN TUFAFI · FALALOLI DA LADUBBA