na rantse da Allah, Allah ya shiryar da mutum daya da kai shi ne mafi alheri daga jajayen …

Musulunci > Ha > Hadith > Likitanci da magani da ta waida ta sharia > na rantse da Allah, Allah ya shiryar da mutum daya da kai shi ne mafi alheri daga jajayen …

Wanda ya ruwaito hadisin: Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi

Ingantacce ne

An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26

📖 Karatu minti 2

Rubutun hadisin: na rantse da Allah, Allah ya shiryar da mutum daya da k…

Bayanin hadisin: na rantse da Allah, Allah ya shiryar da mutum daya da k…

Annabi - tsira da a mincin Allah su tabbata agare shi - ya bai wa sahabbai labari da samun nasarar musulmai akan Yahudawan Khaibara a wayewar gari, hakan ta hannun wani mutum da zai ba shi tuta ne alamar da runduna take rikewa alama a gare ta. Wannan mutumin daga siffofinsa cewa shi yana son Allah da manzonSa, kuma Allah da manzonSa suna sonsa. Sai sahabbai suka kwana suna tunani suna tattaunawa ga wanda za'a bai wa tutar? dan kwaɗayin wannan matsayi mai girma, Lokacin da gari ya waye sai suka tafi zuwa wurin manzon Allah - tsira da a mincin Allah su tabbata agare shi - kowannensu yana kwaɗayin ya rabauta da wannan matsayin,

sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya yi tambaya game da Aliyu ɗan Abu Dalib - Allah Ya yarda da shi -?

sai aka ce : Lallai ba shi da lafiya, yana fama da ciwon idanunsa.

Sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya aika a zo masa da shi, sai ya yi tofi a idon (sayyidina) Aliyu daga yawansu mai daraja, kuma ya yi masa Addu’a, sai ya warke daga cutar kai kace babu wani ciwo a tare da shi, sai ya ba shi tuta, kuma ya umarce shi da zarcewa cikin sauƙi har sai ya yi kusa daga ganuwar maƙiya sai ya bijiro musu da shiga musulunci, idan sun amsa masa; sai ya ba su labari da abinda yake wajaba akansu na farillai.

Sannan tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya bayyanawa Aliyu falalar kira zuwa ga Allah, kuma mai Da'awah idan ya zama sababi a cikin shiriyar wani mutum ɗaya to hakan shi ne mafi alheri a gare shi da ya samu jajayen raƙuman da su ne mafi tsadar dukiyoyin Larabawa, sai ya mallakesu ko ya yi sadaka da su.

Koyarwar hadisin: na rantse da Allah, Allah ya shiryar da mutum daya da k…

Rukunan : LIKITANCI DA MAGANI DA TA-WAIDA TA SHARI'A · FALALOLI · FALALOLIN SAHABBAI ALLAH YA YARDA DA SU · SIRAR ANNABI · FIƘHU DA USULU · YAƘE-YAƘENSA DA YA JE DA KANSA DA WAƊANDA YA AIKA TSIRA DA AMINCIN SU TABBATA A GARESHI · FALALOLI DA LADUBBA · SIRA DA TARIHI

بسم الله الرحمن الرحيم Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
بدر Cikakken Wata Rana 16.6 / 29.5
Haske 96%
Wata Sabo a cikin kwana 13
أستغفر الله Ina neman gafara daga Allah

إِنَّ ٱللَّهَ وَمَلَٰٓئِكَتَهُۥ يُصَلُّونَ عَلَى ٱلنَّبِىِّ ۚ يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ صَلُّوا۟ عَلَيْهِ وَسَلِّمُوا۟ تَسْلِيمًا

Lalle, Allah da malã'ikunSa sunã salati ga Annabi. Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku yi salãti a gare shi, kuma ku yi sallama dõmin amintarwa a gare shi.

Al-Ahzab 33:56

Salati ga Manzon Allah