Kada wani mutum ya kalli al'aurar wani mutum, ko mace ta kalli al'aurar wata mace

Musulunci > Ha > Hadith > Fihun halaye > Kada wani mutum ya kalli al'aurar wani mutum, ko mace ta kalli al'aurar wata mace

Wanda ya ruwaito hadisin: Muslim ne ya rawaito shi

Ingantacce ne

An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26

📖 Karatu minti 1

Rubutun hadisin: Kada wani mutum ya kalli al'aurar wani mutum, ko mace t…

Bayanin hadisin: Kada wani mutum ya kalli al'aurar wani mutum, ko mace t…

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya hana namiji ya kalli al'aurar namiji, ko mace ta kalli al'aurara mace.

Al'aura: Ita ce dukkanin abinda ake jin kunya daga gareshi idan ya bayyana, al'aurar namiji ita ce tsakanin cibiyarsa da gwiwoyinsa, mace dukkaninta al'aurace dangane da maza na nesa, (wadanda akwai aure a tsakanin su) dangane da mata kuwa ko maharramanta to ita zata bayyanar da abinda yake bayyana a al'adance a lokacin aikinta a cikin gida.

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi hani daga kaɗaituwar namiji da namiji a tufafi ɗaya , ko ƙarƙashin mayafi ɗaya alhali suna cikin tsiraici, da kuma mace ta kaɗaita da mace a tufafi ɗaya ko ƙarƙashin mayafi ɗaya a tsiraice; Domin hakan zai iya kaiwa zuwa shafar al'aurar kowanne daga garesu, shafarta kuwa abin hanawa ne, kamar kallon al’amuran ne, kai shi ne ma mafi tsanani a hani; Saboda hakan zai iya kaiwa zuwa barna girma.

Koyarwar hadisin: Kada wani mutum ya kalli al'aurar wani mutum, ko mace t…

Rukunan : FIƘHUN HALAYE · LADUBBA NA SHARI'A · HALAYE ABIN ZARGI · LADUBBAN TUFAFI · FALALOLI DA LADUBBA

بسم الله الرحمن الرحيم Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
بدر Cikakken Wata Rana 16.6 / 29.5
Haske 96%
Wata Sabo a cikin kwana 13
الحمد لله Alhamdulillah - Godiya ta tabbata ga Allah

إِنَّ ٱللَّهَ وَمَلَٰٓئِكَتَهُۥ يُصَلُّونَ عَلَى ٱلنَّبِىِّ ۚ يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ صَلُّوا۟ عَلَيْهِ وَسَلِّمُوا۟ تَسْلِيمًا

Lalle, Allah da malã'ikunSa sunã salati ga Annabi. Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku yi salãti a gare shi, kuma ku yi sallama dõmin amintarwa a gare shi.

Al-Ahzab 33:56

Salati ga Manzon Allah