Musulunci > Ha > Hadith > Alurani mai girma da ilimansa > Yakai baban Al-Munzir, shin ka san wacce aya ce daga littafin Allah mafi girma tare daka…
Ingantacce neAn sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26
📖 Karatu minti 1عَنْ أُبَيِّ بْنِ كَعْبٍ رضي الله عنه قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «يَا أَبَا الْمُنْذِرِ، أَتَدْرِي أَيُّ آيَةٍ مِنْ كِتَابِ اللهِ مَعَكَ أَعْظَمُ؟» قَالَ: قُلْتُ: اللهُ وَرَسُولُهُ أَعْلَمُ. قَالَ: «يَا أَبَا الْمُنْذِرِ، أَتَدْرِي أَيُّ آيَةٍ مِنْ كِتَابِ اللهِ مَعَكَ أَعْظَمُ؟» قَالَ: قُلْتُ: {اللهُ لا إِلَهَ إِلا هُوَ الْحَيُّ الْقَيُّومُ} [البقرة: 255]. قَالَ: فَضَرَبَ فِي صَدْرِي، وَقَالَ: «وَاللهِ لِيَهْنِكَ الْعِلْمُ، أَبَا الْمُنْذِرِ».
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya tambayi Ubayyu Dan Ka'ab game da mafi girman aya a cikin littafin Allah, sai ya yi kai kawo a amsa, sannan ya ce: ita ce Ayatul Kursiyyi: {Allah babu wani abin bautawa da gaskiya sai Shi, Rayayye tabbatacce da kanSa}, sai Annabi -tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya karfafashi, kuma Annabi ya daki kirjinsa dan nuni zuwa cikarsa da ilimi da hikima, kuma ya yi masa addu'a da ya tsira da wannan ilimin kuma ya sawwaka masa shi.
Rukunan : ALƘUR'ANI MAI GIRMA DA ILIMANSA · FALALOLI NA ALƘUR'ANI · FALALOLI · FALALAR ILIMI · FALALOLI NA SURORI DA AYOYI · FALALOLI DA LADUBBA