Zaman dakon yini ɗaya saboda Allah shi ne mafi alheri daga duniya da abinda ke kanta
Musulunci > Ha > Hadith > Fihu na ibada > Zaman dakon yini ɗaya saboda Allah shi ne mafi alheri daga duniya da abinda ke kanta
Wanda ya ruwaito hadisin: Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Ingantacce ne
An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26
📖 Karatu minti 1
Rubutun hadisin: Zaman dakon yini ɗaya saboda Allah shi ne mafi alheri d…
Bayanin hadisin: Zaman dakon yini ɗaya saboda Allah shi ne mafi alheri d…
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labarin cewa lazimtar gurin da yake tsakanin musulmai da kafirai dan gadin musulmai daga gare su a yini ɗaya yana mai tsarkake niyya saboda Allah, shi ne mafi alheri daga duniya da abinda ke cikinta, kuma bigiren bulalar da zai yi yaƙi da ita saboda Allah a cikin aljanna shi ne mafi alheri daga duniya da abinda ke cikinta, kuma lallai cewa lada da sakamakon tafiya a cikin lokaci daga farkon yini zuwa farkon lokacin azahar, ko yammaci: Daga lokacin azahar zuwa dare saboda Allah sau ɗaya, shi ne mafi alheri daga duniya da abinda ke cikinta.
Koyarwar hadisin: Zaman dakon yini ɗaya saboda Allah shi ne mafi alheri d…
- Falalar zaman dako saboda Allah, dan abinda ke cikinsa na sadaukar da rai, dan kuma abinda yake jerantuwa a kansa na ɗaukaka kalmar Allah da taimakon AddininSa; saboda haka lallai sakamakon yini ɗaya, shi ne mafi alheri daga duniya da abinda ke cikinta.
- Wulaƙantar duniya dangane da lahira; domin cewa gurbin bulala na aljanna shi ne mafi alheri daga duniya da abinda ke cikinta.
- Falalar yaƙi saboda Allah, da girman ladansa; domin ladan yammaci ɗaya ko jijjifi ɗaya shi ne mafi alheri daga duniya da abinda ke cikinta.
- Faɗinsa; "Saboda Allah" A cikinsa akwai nuni akan muhimmancin tsarkake niyya, kuma cewa lada mai jerantuwa ne a kansa.
Rukunan :
FIƘHU NA IBADA
· JIHADI
· FALALOLI
· FALALOLIN AYYUKA NAGARI
· FIƘHU DA USULU
· FALALOLI DA LADUBBA
· FALALAR JIHADI
بسم الله الرحمن الرحيم
Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
اللهم صل على محمد
Ya Allah, ka saukar da tsira a kan Muhammad