Babu wani mutum da zai shaida babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma (Annabi) Muhamm…

Musulunci > Ha > Hadith > Ilimin aida > Babu wani mutum da zai shaida babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma (Annabi) Muhamm…

Wanda ya ruwaito hadisin: Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi

Ingantacce ne

An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26

📖 Karatu minti 2

Rubutun hadisin: Babu wani mutum da zai shaida babu abin bautawa da gask…

عن أنس بن مالك رضي الله عنه: أَنَّ النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ وَمُعَاذٌ رَدِيفُهُ عَلَى الرَّحْلِ قَالَ: «يَا مُعَاذُ بْنَ جَبَلٍ»، قَالَ: لَبَّيْكَ يَا رَسُولَ اللهِ وَسَعْدَيْكَ، قَالَ: «يَا مُعَاذُ»، قَالَ: لَبَّيْكَ يَا رَسُولَ اللهِ وَسَعْدَيْكَ، ثَلَاثًا، قَالَ: «مَا مِنْ أَحَدٍ يَشْهَدُ أَنْ لَا إِلَهَ إِلَّا اللهُ وَأَنَّ مُحَمَّدًا رَسُولُ اللهِ صِدْقًا مِنْ قَلْبِهِ إِلَّا حَرَّمَهُ اللهُ عَلَى النَّارِ»، قَالَ: يَا رَسُولَ اللهِ، أَفَلَا أُخْبِرُ بِهِ النَّاسَ فَيَسْتَبْشِرُوا؟ قَالَ: «إِذًا يَتَّكِلُوا». وَأَخْبَرَ بِهَا مُعَاذٌ عِنْدَ مَوْتِهِ تَأَثُّمًا.

Bayanin hadisin: Babu wani mutum da zai shaida babu abin bautawa da gask…

Mu’azu Ɗan Jabal Allah Ya yadda da shi, ya kasance yana bayan Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi a kan abin hawa na dabbarsa, sai ya kira shi Ya Mu’azu, ya maimaita kiran na sa har sau uku, domin ƙarfafawa da Kuma muhimmancin abin zai faɗa masa.

A duka kiran Mu’azu Allah Ya yarda da shi yana amsa masa da cewa; Amsawarka bayan Amsawarka Ya Ma’aikin Allah da da farincin hakan bayan farinciki, Wato na amsa maka Ya Ma’aikin Allah bayan amsawa, kuma na nemi farinciki da wannan amsawa.

Sai Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ba shi bayanin babu wani mutum da zai shaida babu abin bautawa da cancanta sai Allah. Wato; Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma Annabi Muhammad Ma’aikin Allah ne da gaske daga zuciyarsa ba ƙarya ba, idan har ya mutu a wannan hali, to, Allah Ya haramta masa wuta.

Sai Mu’azu Allah Ya yarda da shi ya tambayi Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi a kan ya baiwa mutane labari domin su yi farin ciki su yi wa juna bushara ta alheri?

Sai Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ji tsoron kada su saki jiki da hakan, su ƙaranta ayyuka.

Mu’azu bai ba da wannan bayanin ba sai dab da rasuwarsa, don tsoron kada ya faɗa cikin masu ɓoye ilimi.

Koyarwar hadisin: Babu wani mutum da zai shaida babu abin bautawa da gask…

Rukunan : FALALOLI · FALALOLIN TAUHIDI · ILIMIN AƘIDA · FALALOLI DA LADUBBA · IMANI DA ALLAH MAI GIRMA DA ƊAUKAKA · Kaɗaita Allah cikin Rububiyya

بسم الله الرحمن الرحيم Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
بدر Cikakken Wata Rana 16.5 / 29.5
Haske 97%
Wata Sabo a cikin kwana 13
لا إله إلا الله Babu abin bautawa sai Allah

إِنَّ ٱللَّهَ وَمَلَٰٓئِكَتَهُۥ يُصَلُّونَ عَلَى ٱلنَّبِىِّ ۚ يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ صَلُّوا۟ عَلَيْهِ وَسَلِّمُوا۟ تَسْلِيمًا

Lalle, Allah da malã'ikunSa sunã salati ga Annabi. Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku yi salãti a gare shi, kuma ku yi sallama dõmin amintarwa a gare shi.

Al-Ahzab 33:56

Salati ga Manzon Allah