Ni ina inda zatan bawaNa yake, kuma Ni ina tare da shi lokacin da yake ambatona

Musulunci > Ha > Hadith > Fihun adduoi da zikirai > Ni ina inda zatan bawaNa yake, kuma Ni ina tare da shi lokacin da yake ambatona

Wanda ya ruwaito hadisin: Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi

Ingantacce ne

An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26

📖 Karatu minti 2

Rubutun hadisin: Ni ina inda zatan bawaNa yake, kuma Ni ina tare da shi…

Bayanin hadisin: Ni ina inda zatan bawaNa yake, kuma Ni ina tare da shi…

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa Allah - Maɗaukakin sarki - Yana cewa:

Ni ina inda zatan bawaNa gareNi yake, zan yi mu'amala da bawaNa gwargwadan zatansa da Ni, hakan dan ƙauna da burin rangwami, kuma Ina yi masa abinda yake tinanin afkuwarsa daga gareNi na alheri ne ko wanin hakan; kuma Ni ina tare da shi da rahama da dacewa da shiriya da kiyayewa da ƙarfafawa idan ya anbaceNi.

Idan ya anbaceNi a cikin ransa shi kaɗai a kaɗaice da tasbihi da hailala ko waninsu; zan anbace shi a cikin raiNa.

Idan ya anbaceNi a cikin jama'a; zan ambace shi a cikin jama'ar da tafisu yawa kuma ta fisu tsarki.

Wanda ya nemi kusanci zuwa ga Allah gwargwadan taki Allah Zai yi masa ƙari sai Ya kusanto zuwa gare shi da zira'i.

Idan ya nemi kusanci zuwa gare shi gwargwadan zira'i zai kusanto zuwa gare shi gwargwadan awon faɗin hannaye.

Idan ya zo zuwa ga Allah yana tafiya to Allah zai zo masa Yana sassarfa.

Bawa idan ya nemi kusanci zuwa ga Ubangijinsa da biyayya gareShi da fuskantowa gareShi, to lallai Ubangiji - Maɗaukakin sarki - Zai ƙara kusanci zuwa gareshi dan sakamako daga jinsin aikinsa.

A duk lokacin da bautar mumini ta cika ga Ubangijinsa to Allah Maɗaukakin sarki zai kusanto zuwa gare shi, kyautar Allah da sakamakonSa (ita ce ) mafi yawa daga aikin bawa da kuma wahalarsa, a taƙaice cewa sakamakon Allah mai rinjaya ne akan aiki ta hanyar kaifiyya da kuma kimmiya.

Mumini yana kyautata zato, kuma yana aiki, yana gaggawa yana ƙarawa har ya gamu da Allah.

Koyarwar hadisin: Ni ina inda zatan bawaNa yake, kuma Ni ina tare da shi…

Rukunan : FIƘHUN ADDU'O'I DA ZIKIRAI · ILIMIN AƘIDA · FA'IDOJIN ZIKIRIN ALLAH MAI GIRMA DA ƊAUKAKA · FALALOLI DA LADUBBA · IMANI DA ALLAH MAI GIRMA DA ƊAUKAKA · Kaɗaita Allah cikin sunayenSa da siffofinSa

بسم الله الرحمن الرحيم Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
بدر Cikakken Wata Rana 16.5 / 29.5
Haske 97%
Wata Sabo a cikin kwana 13
اللهم صل على محمد Ya Allah, ka saukar da tsira a kan Muhammad

إِنَّ ٱللَّهَ وَمَلَٰٓئِكَتَهُۥ يُصَلُّونَ عَلَى ٱلنَّبِىِّ ۚ يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ صَلُّوا۟ عَلَيْهِ وَسَلِّمُوا۟ تَسْلِيمًا

Lalle, Allah da malã'ikunSa sunã salati ga Annabi. Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku yi salãti a gare shi, kuma ku yi sallama dõmin amintarwa a gare shi.

Al-Ahzab 33:56

Salati ga Manzon Allah