Shin ɗayanku zai gaza wajen samun kyakykyawan aiki dubu a kowace rana?
Musulunci > Ha > Hadith > Fihun adduoi da zikirai > Shin ɗayanku zai gaza wajen samun kyakykyawan aiki dubu a kowace rana?
Wanda ya ruwaito hadisin: Muslim ne ya rawaito shi
Ingantacce ne
An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26
📖 Karatu minti 1
Rubutun hadisin: Shin ɗayanku zai gaza wajen samun kyakykyawan aiki dubu…
Bayanin hadisin: Shin ɗayanku zai gaza wajen samun kyakykyawan aiki dubu…
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya tambayi sahabbansa: Shin ɗayanku zai iya samun kyakkyawan lada dubu a kowace rana? Sai ɗaya daga cikin mazauna a gurinsa ya ce: Ta yaya mutum zai iya samun kyakkyawan lada dubu a kowace rana cikin sauƙi? Ya ce: To ya ce: "Subhanal Lahi". sau ɗari; sai a rubuta masa kaykkyawa dubu; domin cewa kyakkyawa ɗaya da kwatankwacinsa goma ne, ko kuma a kankare masa mummuna dubu daga cikin munanan ayyukansa.
Koyarwar hadisin: Shin ɗayanku zai gaza wajen samun kyakykyawan aiki dubu…
- Kwaɗaitarwa akan falaloli; domin cewa su ne tsanin ayyukan biyayya.
- Falalar tasbihi da zikiri, kuma cewa wannan aikin mai sauƙi ne wanda mutum ba zai ɗorawa kansa komai ba, da shi ne mutum zai samu wannan ladan mai girma.
- Gaggawar sahabbai zuwa aikata aikin alheri ba tare da wani jinkiri ba.
- Ninka kyawawan ayyuka zuwa kwatankwacinsu sau goma, hakan misalin faɗinSa ne - Allah Maɗaukakin sarki -: (Wanda ya zo da kyakkyawa to yana da kwatankwacinsa goma) [Al-An'am: 160], wannan shi ne mafi ƙarancin matakan ninkawa, inba haka ba ai tabbas haƙiƙa ya zo zuwa ninki ɗari bakwai.
- Ya zo a cikin wasu daga cikin ruwayoyi canjin (Au (ko)) (Wa (da)) a cikin faɗinsa: Ko a sarayar masa... Al-Ƙari ya ce: Wau takan zo da ma'anar Au, dan haka babu saɓani tsakanin ruwayoyi biyun, kamar ma'ana: Cewa wanda ya faɗeta za'a rubuta masa kyakkyawa dubu, idan bai zamo a kansa ba sai a sarayar masa da wani abu a kuma ba shi wani abu, kuma zai iya yi wuwa Au ɗin ta kasance da ma'anar Wau, ko da ma'anar kai, to a wannan lokacin sai a haɗa tsakaninsu, kuma falalar Allah ta fi yalwa daga hakan ya ƙare, cewa shi za'a rubuta masa kyawawan lada dubu kuma a sarayar masa da munanan ayyuka dubu.
Rukunan :
FIƘHUN ADDU'O'I DA ZIKIRAI
· FA'IDOJIN ZIKIRIN ALLAH MAI GIRMA DA ƊAUKAKA
· FALALOLI DA LADUBBA
بسم الله الرحمن الرحيم
Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
لا إله إلا الله
Babu abin bautawa sai Allah