Wannan wani Sahiɗan ne ana ce masa khinzab, idan ka ji shi ka nemi tsarin Allah daga gare…

Musulunci > Ha > Hadith > Ilimin aida > Wannan wani Sahiɗan ne ana ce masa khinzab, idan ka ji shi ka nemi tsarin Allah daga gare…

Wanda ya ruwaito hadisin: Muslim ne ya rawaito shi

Ingantacce ne

An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26

📖 Karatu minti 1

Rubutun hadisin: Wannan wani Sahiɗan ne ana ce masa khinzab, idan ka ji…

عن عُثْمَانَ بْنَ أَبِي الْعَاصِ رضي الله عنه: أنه أَتَى النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ فَقَالَ: يَا رَسُولَ اللهِ، إِنَّ الشَّيْطَانَ قَدْ حَالَ بَيْنِي وَبَيْنَ صَلَاتِي وَقِرَاءَتِي يَلْبِسُهَا عَلَيَّ، فَقَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «ذَاكَ شَيْطَانٌ يُقَالُ لَهُ خِنْزَِبٌ، فَإِذَا أَحْسَسْتَهُ فَتَعَوَّذْ بِاللهِ مِنْهُ، وَاتْفُلْ عَلَى يَسَارِكَ ثَلَاثًا»، قَالَ: فَفَعَلْتُ ذَلِكَ فَأَذْهَبَهُ اللهُ عَنِّي.

Bayanin hadisin: Wannan wani Sahiɗan ne ana ce masa khinzab, idan ka ji…

Usman ɗan Abul Aas - Allah Ya yarda da shi - ya zo wurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - sai ya ce: Ya Manzon Allah lallai cewa Shaiɗan haƙiƙa ya shiga tsakanina da sallata ya hanani khushu'i a cikinta, ya cakuɗa min karatuna ya sa ni kokwanto a cikinta, Sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: Wannan Shaiɗan ne ana ce masa Khinzab, idan ka ka sami hakan, kuma ka ji shi ka nemi mafaka a wurin Allah, ka nemi tsarin Allah daga gare Shi, ka yi tofi a hagunka tare da yawu kaɗan sau uku, Usman ya ce: Sai na aikata abin da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya umarce ni da shi, sai Allah Ya tafiyar da shi daga gareni.

Koyarwar hadisin: Wannan wani Sahiɗan ne ana ce masa khinzab, idan ka ji…

Rukunan : FIƘHU NA IBADA · SALLAH · FALALOLI · FIƘHUN ADDU'O'I DA ZIKIRAI · FALALOLIN ZIKIRI · ILIMIN AƘIDA · ZIKIRAI NA AL'AMURA MASU BIJIROWA · FIƘHU DA USULU · SIFFAR SALLAH · FALALOLI DA LADUBBA · IMANI DA MALA'IKU · ALJANU

بسم الله الرحمن الرحيم Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
بدر Cikakken Wata Rana 16.5 / 29.5
Haske 97%
Wata Sabo a cikin kwana 13
اللهم صل على محمد Ya Allah, ka saukar da tsira a kan Muhammad

إِنَّ ٱللَّهَ وَمَلَٰٓئِكَتَهُۥ يُصَلُّونَ عَلَى ٱلنَّبِىِّ ۚ يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ صَلُّوا۟ عَلَيْهِ وَسَلِّمُوا۟ تَسْلِيمًا

Lalle, Allah da malã'ikunSa sunã salati ga Annabi. Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku yi salãti a gare shi, kuma ku yi sallama dõmin amintarwa a gare shi.

Al-Ahzab 33:56

Salati ga Manzon Allah