Musulunci > Ha > Hadith > Fihun halaye > 'Lallai Ni na san wata kalmar da zai faɗeta da abinda yake ji ya tafi daga gare shi, da za…
Ingantacce neAn sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26
📖 Karatu minti 1wasu mutane biyu sun yi zage-zage a gaban Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, alhali fuskar ɗayansu ta yi jā, jijiyoyinsa da suka kewaye wuyansa sun kunbura.
Sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: Lallai ni na san kalmar da wannan mai fushin zai faɗeta da fushin ya tafi daga gare shi, da zai ce: Ina neman tsarin Allah daga Shaiɗan abin jefewa.
Sai suka ce masa: Lallai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: Ka nemi tsarin Allah daga Shaiɗan.
Sai ya ce: Shin ni mahaukaci ne? ya yi zatan cewa ba mai neman tsari daga Shaiɗan sai wanda yake da hauka.
Rukunan : FIƘHUN HALAYE · FIƘHUN ADDU'O'I DA ZIKIRAI · HALAYE ABIN ZARGI · ZIKIRAI NA AL'AMURA MASU BIJIROWA · FALALOLI DA LADUBBA