Da a ce ɗan Adam yana da kwari biyu na dukiya da sai ya nemi wani kwarin na uku
Musulunci > Ha > Hadith > Fihun halaye > Da a ce ɗan Adam yana da kwari biyu na dukiya da sai ya nemi wani kwarin na uku
Wanda ya ruwaito hadisin: Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Ingantacce ne
An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26
📖 Karatu minti 1
Rubutun hadisin: Da a ce ɗan Adam yana da kwari biyu na dukiya da sai ya…
Bayanin hadisin: Da a ce ɗan Adam yana da kwari biyu na dukiya da sai ya…
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa da a ce ɗan Adam zai samu wani kwari cike da zinari, da zai so saboda kwaɗayinsa wanda shi ne ɗabi'arsa ta zama yana da wasu kwari biyun daban, kuma cewa shi ba zai gushe ba yana kwaɗayi akan duniya har sai ya mutu cikinsa ya cika da ƙasar ƙabarinsa.
Koyarwar hadisin: Da a ce ɗan Adam yana da kwari biyu na dukiya da sai ya…
- Tsananin kwaɗayin mutum akan tara dukiya da waninta na kayan jin daɗin rayuwar duniya.
- Nawawi ya ce: A cikinsa akwai zargin kwaɗayi akan duniya da kuma son tara dukiya a cikinta da kuma kwaɗayinta.
- Allah - Maɗaukakin sarki - Yana karɓar tuban wanda ya tuba daga siffofi ababan zargi.
- Nawai ya ce: Hadisin ya zo ne akan hukuncin mafi yawancin mutane a kan kwaɗayin duniya, kuma faɗinsa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: (Allah Yana karɓar tuban wanda ya tuba) yana ƙarfafarsa.
Rukunan :
FIƘHUN HALAYE
· ABUBUWA MASU TAUSASA ZUKATA DA WA'AZOZI
· HALAYE ABIN ZARGI
· ZARGIN SON DUNIYA
· FALALOLI DA LADUBBA
بسم الله الرحمن الرحيم
Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
اللهم صل على محمد
Ya Allah, ka saukar da tsira a kan Muhammad