Bai kasance mai yawan alfasha ba, ko mai yawan ɗorawa kansa alfasha ba, ko mai kwararoto a…
Musulunci > Ha > Hadith > Fihun halaye > Bai kasance mai yawan alfasha ba, ko mai yawan ɗorawa kansa alfasha ba, ko mai kwararoto a…
Wanda ya ruwaito hadisin: Tirmizi da Ahmad sun rawaito shi
Ingantacce ne
An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26
📖 Karatu minti 1
Rubutun hadisin: Bai kasance mai yawan alfasha ba, ko mai yawan ɗorawa k…
Bayanin hadisin: Bai kasance mai yawan alfasha ba, ko mai yawan ɗorawa k…
An tambayi Uwar muminai Nana A'isha - Allah Ya yarda da ita - game da ɗabi'un Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sai ta ce: Alfasha da munanan maganganu ko ayyuka ba su zama daga ɗabi'unsa ba, kuma ba ya ɗorawa kansa alfasha, kuma ba ya yi da gangan, kuma ba ya ihu yana ɗaga muryarsa a cikin kasuwanni, kuma ba ya rama mummuna da mummuna, sai dai yana sakayya da kyakkyawa, kuma yana yin afuwa a baɗini, kuma yana kau da kai yana kawar dakai a zahiri.
Koyarwar hadisin: Bai kasance mai yawan alfasha ba, ko mai yawan ɗorawa k…
- Bayanin abinda Annabi - tsira da amincin Allah su tabbat agare shi - yake a kansa na manyan ɗabi'u, da nisanta daga ɗabi'u ababen zargi.
- Kwaɗaitarwa akan aikata kyawawan ɗabi'u da kuma nisantar munanan ɗabi'u.
- Zargin yin magana da munananawa a magana da kuma mummunan zance.
- Zargin ɗaga murya ga mutane dayi musu ihu.
- Kwaɗaitarwa akan rama mummuna da kyakkyawan abu da kuma yin afuwa da kau da kai.
Rukunan :
FIƘHUN HALAYE
· HALAYE NAGARI
· SIRAR ANNABI
· ƊABI'U IRIN NA (ANNABI) MUHAMMAD
· FALALOLI DA LADUBBA
· SIFFOFINSA NA HALITTA
· AFUWARSA TSIRA DA AMINCIN ALLAH SU TABBATA A GARESHI
· SIRA DA TARIHI
بسم الله الرحمن الرحيم
Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
حسبنا الله ونعم الوكيل
Allah Ya isa mana, Shi ne mafi kyawun Mai Kiyaye