Wani bawa ba zai suturta wani bawa a duniya ba sai Allah Ya suturta shi a ranar Alƙiyama
Musulunci > Ha > Hadith > Fihun halaye > Wani bawa ba zai suturta wani bawa a duniya ba sai Allah Ya suturta shi a ranar Alƙiyama
Wanda ya ruwaito hadisin: Muslim ne ya rawaito shi
Ingantacce ne
An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26
📖 Karatu minti 1
Rubutun hadisin: Wani bawa ba zai suturta wani bawa a duniya ba sai Alla…
Bayanin hadisin: Wani bawa ba zai suturta wani bawa a duniya ba sai Alla…
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bayyana cewa wani musulmi ba zai suturta ɗan uwansa musulmi ba a cikin wani al'amari daga al'amura, sai Allah - Mai girma da ɗaukaka - Ya suturta shi a ranar alƙiyama; sakayya tana daga jinsin aiki, kuma suturcewar Allah gare shi zai zama da suturcewar laifukansa da saɓonsa daga yaɗasu ga ma'abota taron alƙiyama, zai iya kasancewa da barin yi masa hisabi akansu da kuma anbata masa su.
Koyarwar hadisin: Wani bawa ba zai suturta wani bawa a duniya ba sai Alla…
- Halaccin rufawa musulmi asiri idan ya aikata wani saɓo, tare da yin inkari akansa da kuma yi masa nasiha, da tsoratar da shi Allah, amma idan ya kasance daga ma'abota sharri da ɓarna ne masu bayyana saɓo da fasiƙanci, to cewa shi ba ya kamata a rufa musu asiri; domin rufa musu asiri zai sa su ƙarfin hali akan saɓo, kawai ana ɗaga al'amarinsa ne zuwa ga hukuma, koda a hakan akwai anbatansa; domin cewa shi mai bayyanar da fasiƙancinsa ne da kuma saɓonsa.
- Kwaɗaitarwa a kan rufa asirin kurakuren wasu.
- Daga fa'idojin rufa asiri: Bada dama ga mai yin zunubi ya yi tinani kuma ya tuba zuwa ga Allah; domin bayyanar da aibuka da al'aurori yana daga yayata alfasha, kuma yana ɓata yanayin zamantakewa, kuma yana ruɗar mutane da aikata su.
Rukunan :
FIƘHUN HALAYE
· HALAYE NAGARI
· ILIMIN AƘIDA
· FALALOLI DA LADUBBA
· IMANI DA ALLAH MAI GIRMA DA ƊAUKAKA
· Kaɗaita Allah cikin sunayenSa da siffofinSa
بسم الله الرحمن الرحيم
Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
اللهم صل على محمد
Ya Allah, ka saukar da tsira a kan Muhammad