Kada ku wuce gona da iri wajen yabona, yadda Nasara suka maida Dan Maryam, ni kawai bawa n…
Musulunci > Ha > Hadith > Ilimin aida > Kada ku wuce gona da iri wajen yabona, yadda Nasara suka maida Dan Maryam, ni kawai bawa n…
Wanda ya ruwaito hadisin: Bukhari ne ya rawaito shi
Ingantacce ne
An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26
📖 Karatu minti 1
Rubutun hadisin: Kada ku wuce gona da iri wajen yabona, yadda Nasara suk…
عَن عُمَرَ بنِ الخَطَّابِ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ قال: سَمِعْتُ النَّبِيَّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَقُولُ: «لَا تُطْرُونِي كَمَا أَطْرَتِ النَّصَارَى ابْنَ مَرْيَمَ؛ فَإِنَّمَا أَنَا عَبْدُهُ، فَقُولُوا: عَبْدُ اللهِ وَرَسُولُهُ».
Bayanin hadisin: Kada ku wuce gona da iri wajen yabona, yadda Nasara suk…
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana hani daga wuce gona da iri da kuma ketare iyakar shari'a a yabonsa da kuma siffanta shi da siffofin Allah - Madaukakin sarki - da kuma ayyukansa wadanda suka kebanta da shi, ko cewa shi yana sanin gaibu, ko a kira shi tare da Allah, kamar yadda Nasara suka aikata tare da Isa Dan Maryam - amincin Allah ya tabbata a gare shi -. Sannan ya bayyana cewa shi bawa ne daga bayin Allah, ya kuma yi umarni da mu fada game da shi: Bawan Allah kuma ManzonSa.
Koyarwar hadisin: Kada ku wuce gona da iri wajen yabona, yadda Nasara suk…
- Gargadarwa daga ketare iyakar shari'a a girmamawa da yabo; domin cewa hakan yana kaiwa zuwa ga shirka.
- Abinda Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya yi gargadi akan sa ya afku a cikin wannan al'ummar, sai wasu mutane suka wuce gona da iri a Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, wasu mutanen kuma a iyalan gidansa, wasu mutanen kuma a waliyyai, sai suka fada a cikin shirka.
- Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya siffanta kansa da cewa shi bawan Allah ne; dan ya bayyana cewa shi bawa ne wanda yake bauta ga Allah, ba ya halatta a juyar masa da wani abu daga abinda Ubangiji Ya kebanta da shi.
- Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya siffanta kansa da cewa shi Manzon Allah ne abin aikowa daga wurin Allah to gasgata shi da binsa ya wajaba.
Rukunan :
ILIMIN AƘIDA
· IMANI DA ALLAH MAI GIRMA DA ƊAUKAKA
· Kaɗaita Allah cikin bauta
بسم الله الرحمن الرحيم
Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
الله أكبر
Allah Shi ne Mafi Girma