Akan me zamu yi maka caffa? ya ce: "Akan ku bautawa Allah kuma kada ku sanya wa Allah wan…

Musulunci > Ha > Hadith > Ilimin aida > Akan me zamu yi maka caffa? ya ce: "Akan ku bautawa Allah kuma kada ku sanya wa Allah wan…

Wanda ya ruwaito hadisin: Muslim ne ya rawaito shi

Ingantacce ne

An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26

📖 Karatu minti 1

Rubutun hadisin: Akan me zamu yi maka caffa? ya ce: "Akan ku bautawa Al…

عَنْ أَبِي مُسْلِمٍ الْخَوْلَانِيِّ، قَالَ: حَدَّثَنِي الْحَبِيبُ الْأَمِينُ، أَمَّا هُوَ فَحَبِيبٌ إِلَيَّ، وَأَمَّا هُوَ عِنْدِي فَأَمِينٌ، عَوْفُ بْنُ مَالِكٍ الْأَشْجَعِيُّ رضي الله عنه قَالَ: كُنَّا عِنْدَ رَسُولِ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، تِسْعَةً أَوْ ثَمَانِيَةً أَوْ سَبْعَةً، فَقَالَ: «أَلَا تُبَايِعُونَ رَسُولَ اللهِ؟» وَكُنَّا حَدِيثَ عَهْدٍ بِبَيْعَةٍ، فَقُلْنَا: قَدْ بَايَعْنَاكَ يَا رَسُولَ اللهِ، ثُمَّ قَالَ: «أَلَا تُبَايِعُونَ رَسُولَ اللهِ؟» فَقُلْنَا: قَدْ بَايَعْنَاكَ يَا رَسُولَ اللهِ، ثُمَّ قَالَ: «أَلَا تُبَايِعُونَ رَسُولَ اللهِ؟» قَالَ: فَبَسَطْنَا أَيْدِيَنَا وَقُلْنَا: قَدْ بَايَعْنَاكَ يَا رَسُولَ اللهِ، فَعَلَامَ نُبَايِعُكَ؟ قَالَ: «عَلَى أَنْ تَعْبُدُوا اللهَ وَلَا تُشْرِكُوا بِهِ شَيْئًا، وَالصَّلَوَاتِ الْخَمْسِ، وَتُطِيعُوا -وَأَسَرَّ كَلِمَةً خَفِيَّةً- وَلَا تَسْأَلُوا النَّاسَ شَيْئًا» فَلَقَدْ رَأَيْتُ بَعْضَ أُولَئِكَ النَّفَرِ يَسْقُطُ سَوْطُ أَحَدِهِمْ، فَمَا يَسْأَلُ أَحَدًا يُنَاوِلُهُ إِيَّاهُ.

Bayanin hadisin: Akan me zamu yi maka caffa? ya ce: "Akan ku bautawa Al…

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance a cikin wani adadi na sahabbai sai ya nemi su yi masa caffa su yi masa alkawari akan lazimtar wasu al'amura har sau uku:

Na farko: Bautar Allah Shi kadai ta hanyar riko da umarninSa, da nisantar haninSa, kuma kada su hada wani abu daShi.

Na biyu: Tsaida salloli biyar na wajibai a yini da dare.

Na uku: Ji da bi da aikin alheri ga wanda ya jibinci al'amarin musulmai.

Na hudu: Kai dukkanin bukatunsu ga Allah da rashin tambayar mutane wani abu daga garesu, Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi kasa-kasa da sautinsa da su.

Hakika sahabbai - Allah Ya yarda da su - sun yi aiki da abinda suka yi caffa akansa, har maruwaicin Hadisin ya ce: Hakika na ga wasu daga wadancan sahabban bulalar dayansu tana faduwa kasa , amma ba ya tambayar wani ya miko masa ita, kai yana sauka yana daukarta da kansa.

Koyarwar hadisin: Akan me zamu yi maka caffa? ya ce: "Akan ku bautawa Al…

Rukunan : ILIMIN AƘIDA · IMANI DA ALLAH MAI GIRMA DA ƊAUKAKA · Kaɗaita Allah cikin bauta

بسم الله الرحمن الرحيم Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
بدر Cikakken Wata Rana 16.6 / 29.5
Haske 96%
Wata Sabo a cikin kwana 13
لا إله إلا الله Babu abin bautawa sai Allah

إِنَّ ٱللَّهَ وَمَلَٰٓئِكَتَهُۥ يُصَلُّونَ عَلَى ٱلنَّبِىِّ ۚ يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ صَلُّوا۟ عَلَيْهِ وَسَلِّمُوا۟ تَسْلِيمًا

Lalle, Allah da malã'ikunSa sunã salati ga Annabi. Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku yi salãti a gare shi, kuma ku yi sallama dõmin amintarwa a gare shi.

Al-Ahzab 33:56

Salati ga Manzon Allah