Yakai ɗan Adam lallai cewa kai baka roƙeni ba, ka yi kwaɗayi gareni zan gafarta maka abind…
Musulunci > Ha > Hadith > Ilimin aida > Yakai ɗan Adam lallai cewa kai baka roƙeni ba, ka yi kwaɗayi gareni zan gafarta maka abind…
Wanda ya ruwaito hadisin: Tirmizi ne ya ruwaito shi
Hasan ne
An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26
📖 Karatu minti 1
Rubutun hadisin: Yakai ɗan Adam lallai cewa kai baka roƙeni ba, ka yi kw…
عَنْ أَنَسِ بْنِ مَالِكٍ رضي الله عنه قَالَ: سَمِعْتُ رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَقُولُ: «قَالَ اللَّهُ تَبَارَكَ وَتَعَالَى: يَا ابْنَ آدَمَ إِنَّكَ مَا دَعَوْتَنِي وَرَجَوْتَنِي غَفَرْتُ لَكَ عَلَى مَا كَانَ فِيكَ وَلاَ أُبَالِي، يَا ابْنَ آدَمَ لَوْ بَلَغَتْ ذُنُوبُكَ عَنَانَ السَّمَاءِ ثُمَّ اسْتَغْفَرْتَنِي غَفَرْتُ لَكَ، وَلاَ أُبَالِي، يَا ابْنَ آدَمَ إِنَّكَ لَوْ أَتَيْتَنِي بِقُرَابِ الأَرْضِ خَطَايَا ثُمَّ لَقِيتَنِي لاَ تُشْرِكُ بِي شَيْئًا لأَتَيْتُكَ بِقُرَابِهَا مَغْفِرَةً».
Bayanin hadisin: Yakai ɗan Adam lallai cewa kai baka roƙeni ba, ka yi kw…
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labari cewa Allah - alherinSa ya yawaita kuma Ya ɗaukaka - Ya faɗa a cikin hadisi Kudisi:
Ya kai ɗan Adam muddin dai kana roƙoNa kana kwaɗayin rahamata, ba ka yanke ƙauna ba; zan suturta zunubanka zan shafesu batare da kulawa ba a cikinsu; koda wannan zunubin da sabon sun kasance daga manyan zunubai ne. Ya kai ɗan Adam ! Da zunubanka sun yawaita yawan da zasu cika abinda ke tsakanin sama da ƙasa ta inda suka kai sasanninta kuma suka game gefanta, sannan ka nemi gafarata; zan shafe zan gafarta maka dukkaninsu ba tare da kulawa da yawansu ba.
Ya kai ɗan Adam: Lallai kai da zaka zo min bayan mutuwa da zunubai da sabo cikin ƙasa, kuma ka zama mai tauhidi baka taranya wani abu daNi ba; dana fuskanci waɗannan zunuban da sabon da gafara cikin ƙasa; domin cewa Ni Mai yalwar gafar ne, kuma ina gafarta dukkan zunubai in banda shirka.
Koyarwar hadisin: Yakai ɗan Adam lallai cewa kai baka roƙeni ba, ka yi kw…
- Yalwar rahamar Allah - Maɗaukakin sarki - da gafararSa da falalarSa.
- Falalar Tauhidi, kuma cewa Allah Yana gafarta zunubai da sabo ga masu Tauhidi.
- Haɗarin shirka kuma cewa Allah ba Ya gafara ga masu shirka.
- Ibnu Rajab ya ce: Haƙiƙa wannan Hadisin ya ƙunshi sabubba uku waɗanda gafarta zunubai suke samuwa da su: Na farko: Addu'a tare da ƙauna. Na biyu: Istgfari da neman tuba. Na uku: Mutuwa akan Tauhidi.
- Wannan Hadisin yana daga abin da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yake ruwaito shi daga Ubangijinsa, ana ambatonsa da Hadisi Ƙudsi, ko Ilahi, shi ne wanda lafazinsa da ma'anarsa daga Allah ne, sai dai shi babu keɓance-keɓancen Alƙur’ani a cikinsa waɗanda ya keɓanta da su daga waninsa, kamar bauta da karanta shi, da yin alwala sabo da taba shi da fito na fito(ƙalubalanta) da gajiyarwa, (Mu’ujiza) da sauransu.
- Zunubai nau'i uku ne: Na farko: Shirka da Allah; wannan Allah ba Ya gafarta shi, Allah - Mai girma da ɗaukaka - Ya ce: {Lallai cewa shi wanda ya yi shirka da Allah to haƙiƙa Allah Ya haramta masa aljanna}. Na biyu: Zalintar bawa ga kansa a cikin abinda ke tsakaninsa da tsakanin Ubangijinsa na zunubai da sabo; domin cewa Allah - Mai girma da ɗaukaka - zai gafarta hakan, kuma zai ƙetare in Ya so. Na uku: Zunuban da Allah baYa barin komai daga garesu; su ne zalintar bayi sashinsu da sashi, babu makawa daga sakayya.
Rukunan :
ABUBUWA MASU TAUSASA ZUKATA DA WA'AZOZI
· ILIMIN AƘIDA
· TUBA
· FALALOLI DA LADUBBA
· IMANI DA ALLAH MAI GIRMA DA ƊAUKAKA
· Kaɗaita Allah cikin sunayenSa da siffofinSa
بسم الله الرحمن الرحيم
Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
أستغفر الله
Ina neman gafara daga Allah