Wanda ya ya yi gaba da masoyiNa to na yi shelar yaki da shi, kuma bawaNa bai taba kusanta …

Musulunci > Ha > Hadith > Ilimin aida > Wanda ya ya yi gaba da masoyiNa to na yi shelar yaki da shi, kuma bawaNa bai taba kusanta …

Wanda ya ruwaito hadisin: Bukhari ne ya rawaito shi

Ingantacce ne

An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26

📖 Karatu minti 2

Rubutun hadisin: Wanda ya ya yi gaba da masoyiNa to na yi shelar yaki da…

عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «إِنَّ اللَّهَ قَالَ: مَنْ عَادَى لِي وَلِيًّا فَقَدْ آذَنْتُهُ بِالحَرْبِ، وَمَا تَقَرَّبَ إِلَيَّ عَبْدِي بِشَيْءٍ أَحَبَّ إِلَيَّ مِمَّا افْتَرَضْتُ عَلَيْهِ، وَمَا يَزَالُ عَبْدِي يَتَقَرَّبُ إِلَيَّ بِالنَّوَافِلِ حَتَّى أُحِبَّهُ، فَإِذَا أَحْبَبْتُهُ: كُنْتُ سَمْعَهُ الَّذِي يَسْمَعُ بِهِ، وَبَصَرَهُ الَّذِي يُبْصِرُ بِهِ، وَيَدَهُ الَّتِي يَبْطِشُ بِهَا، وَرِجْلَهُ الَّتِي يَمْشِي بِهَا، وَإِنْ سَأَلَنِي لَأُعْطِيَنَّهُ، وَلَئِنِ اسْتَعَاذَنِي لَأُعِيذَنَّهُ، وَمَا تَرَدَّدْتُ عَنْ شَيْءٍ أَنَا فَاعِلُهُ تَرَدُّدِي عَنْ نَفْسِ المُؤْمِنِ، يَكْرَهُ المَوْتَ وَأَنَا أَكْرَهُ مَسَاءَتَهُ».

Bayanin hadisin: Wanda ya ya yi gaba da masoyiNa to na yi shelar yaki da…

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin a cikin Hadisi Kudsi cewa Allah - Mai girma da daukaka - Ya ce: Wanda ya cutar da wani masoyi daga masoyana ya fusatar da shi ya ki shi to hakika Na sanar da shi na shelanta masa kiyayya.

Waliyyi shi ne: Mumini mai tsoron Allah, kuma gwargwadan abinda ke ga bawa na imani da tsoron Allah rabonsa na walicci yake kasancewa. Musulmi bai nemi kusanci ga Ubangijinsa ba da wani abu daga abinda Ya fi soyuwa gare Shi kamar wanda ya wajabta masa na aikata biyayya da barin abubuwan da aka haramta, kuma musulmi ba zai gushe ba yana kara kusanci ga Ubangijinsa da nafilfili tare da farillai ba; Har sai ya samu soyayyar Allah. Idan Allah Ya so shi, to Allah Zai zama Mai daidaita shi a wadannan gabobin guda hudu:

Zai daidaita shi a jinsa, ba zai ji komai ba sai abinda Allah Ya yarda da shi.

Kuma Zai daidaita shi a ganinsa, ba zai kalli komai ba sai abinda Allah Yake son kallo zuwa gare shi kuma Ya yarda da shi.

Kuma Zai daidaita shi a hannunsa, ba zai aikata komai da hannunsa ba sai abinda zai yardar da Allah.

Kuma Zai daidaita shi a kafarsa, ba zai yi tafiya ba sai inda zai yardar da Allah, kuma ba zai yi wani kokari ba sai abinda acikinsa akwai alheri.

A tare da hakan idan ya roki Allah wani abu to lallai Allah zai ba shi abinda ya roka, sai ya zama wanda ake amsawa addu'a, idan ya nemi tsarin Allah ya fake gareShi dan neman tsari, to cewa Allah Zai tsare shi Zai kare shi daga abinda yake jin tsoro.

Sannan Allah - Madaukakin sarki - Ya ce: Ban yi wani kai kawo ba game da wani abu da Ni zan aikata shi ba kamar kaikawo Na a karbar ran mumini dan tausayinsa; Domin shi yana kin mutuwa, dan abinda ke cikinta na radadi, Allah kuma Yana kin abinda zaisa mumini jin radadi.

Koyarwar hadisin: Wanda ya ya yi gaba da masoyiNa to na yi shelar yaki da…

Rukunan : ILIMIN AƘIDA · IMANI DA ALLAH MAI GIRMA DA ƊAUKAKA · Kaɗaita Allah cikin sunayenSa da siffofinSa

بسم الله الرحمن الرحيم Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
بدر Cikakken Wata Rana 16.6 / 29.5
Haske 96%
Wata Sabo a cikin kwana 13
لا حول ولا قوة إلا بالله Babu wata ƙarfi ko iko sai na Allah

إِنَّ ٱللَّهَ وَمَلَٰٓئِكَتَهُۥ يُصَلُّونَ عَلَى ٱلنَّبِىِّ ۚ يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ صَلُّوا۟ عَلَيْهِ وَسَلِّمُوا۟ تَسْلِيمًا

Lalle, Allah da malã'ikunSa sunã salati ga Annabi. Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku yi salãti a gare shi, kuma ku yi sallama dõmin amintarwa a gare shi.

Al-Ahzab 33:56

Salati ga Manzon Allah