Musulunci > Ha > Hadith > Ilimin aida > Ka fadamin wata magana a Musulunci da ba zan tambayi waninka game da ita ba, ya ce: "Ka ce…
Ingantacce neAn sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26
📖 Karatu minti 1عَنْ سُفْيان بنِ عَبْدِ اللهِ الثَّقَفِيّ رضي الله عنه قال: قُلْتُ: يَا رَسُولَ اللهِ، قُلْ لِي فِي الْإِسْلَامِ قَوْلًا لَا أَسْأَلُ عَنْهُ أَحَدًا غَيْرَكَ، قَالَ: «قُلْ: آمَنْتُ بِاللهِ، ثُمَّ اسْتَقِمْ».
Sahabi Sufayanu dan Abdullahi - Allah Ya yarda da shi - ya tambayi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da ya sanar da shi wata magana mai tattaro ma'anonin Musulunci, da zai yi riko da ita, wacce ba zai tambayi waninsa game da ita ba? Sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: Ka ce: Na kadaita Allah, kuma na yi imani da cewa Shi ne Ubangijina kuma Allah na, Mahaliccina, Abin bautata na gaskiya ba Shi da abokin tarayya, Sannan ya jawu ga biyayya ga Allah ta hanyar bada farillan Allah, da barin abubuwan da Allah Ya haramta, ya kuma ci gaba akansu.
Rukunan : ABUBUWA MASU TAUSASA ZUKATA DA WA'AZOZI · ILIMIN AƘIDA · TSARKAKE ZUKATA · FALALOLI DA LADUBBA · IMANI DA ALLAH MAI GIRMA DA ƊAUKAKA