Lallai cewa Allah zai tseratar da wani mutum daga al'ummata agaban halittu a ranar Alkiyam…

Musulunci > Ha > Hadith > Ilimin aida > Lallai cewa Allah zai tseratar da wani mutum daga al'ummata agaban halittu a ranar Alkiyam…

Wanda ya ruwaito hadisin: Tirmizi ne ya Rawaito shi

Ingantacce ne

An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26

📖 Karatu minti 2

Rubutun hadisin: Lallai cewa Allah zai tseratar da wani mutum daga al'um…

عَنْ عَبْدِ اللهِ بْنِ عَمْرِو بْنِ العَاصِ رضي الله عنهما قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «إِنَّ اللهَ سَيُخَلِّصُ رَجُلًا مِنْ أُمَّتِي عَلَى رُءُوسِ الْخَلَائِقِ يَوْمَ الْقِيَامَةِ، فَيَنْشُرُ عَلَيْهِ تِسْعَةً وَتِسْعِينَ سِجِلًّا، كُلُّ سِجِلٍّ مِثْلُ مَدِّ الْبَصَرِ، ثُمَّ يَقُولُ: أَتُنْكِرُ مِنْ هَذَا شَيْئًا؟ أَظَلَمَكَ كَتَبَتِي الْحَافِظُونَ؟ فَيَقُولُ: لَا يَا رَبِّ، فَيَقُولُ: أَفَلَكَ عُذْرٌ؟ فَيَقُولُ: لَا يَا رَبِّ، فَيَقُولُ: بَلَى إِنَّ لَكَ عِنْدَنَا حَسَنَةً، فَإِنَّهُ لَا ظُلْمَ عَلَيْكَ الْيَوْمَ، فَتُخْرَجُ بِطَاقَةٌ فِيهَا: أَشْهَدُ أَنْ لَا إِلَهَ إِلَّا اللهُ وَأَشْهَدُ أَنَّ مُحَمَّدًا عَبْدُهُ وَرَسُولُهُ، فَيَقُولُ: احْضُرْ وَزْنَكَ، فَيَقُولُ: يَا رَبِّ مَا هَذِهِ الْبِطَاقَةُ مَعَ هَذِهِ السِّجِلَّاتِ؟ فَقَالَ: إِنَّكَ لَا تُظْلَمُ، قَالَ: فَتُوضَعُ السِّجِلَّاتُ فِي كِفَّةٍ، وَالْبِطَاقَةُ فِي كِفَّةٍ، فَطَاشَتِ السِّجِلَّاتُ، وَثَقُلَتِ الْبِطَاقَةُ، فَلَا يَثْقُلُ مَعَ اسْمِ اللهِ شَيْءٌ».

Bayanin hadisin: Lallai cewa Allah zai tseratar da wani mutum daga al'um…

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa Allah Zai zabi wani mutum daga al'ummarsa agaban halittu , za'a kira shi dan a yi masa hisabi, sai (Ubangiji) ya bijiro masa da fayilillika casa'in da tara, su ne takardun ayyukansa wadanda ya kasance yana aikatasu a duniya, kuma tsawon kowane fayil tamkar iya ganinnka ne. Sannan Allah - mai girma da daukaka - ya cewa wannan mutumin: Shin kana musun wani abu daga abinda aka rubuta a cikin wadanannan fayilillikan? Shin Mala'ikuna masu kiyayewa masu rubutu sun zalinceka?. Sai mutumin ya ce: A'a ya Ubangiji. Sai Allah - mai girma da daukaka - ya ce: Shin kana da wani hanzari da za'a yi maka uzuri da shi daga abinda ka gabatar na ayyuka a duniya? daga kasancewarsa rafkanuwa ne, ko kuskurene ko jahilcine, Sai mutumin ya ce: A'a ya Ubangiji ba ni da wani hanzari. Sai Allah - mai girma da daukaka - ya ce: Eh, lallai kana da wani kyakkyawan aiki a wurinMu, kuma cewa babu wani zalinci akanka a yau. Ya ce: Sai a fitar da wani kati an rubutawa a ciki: Ina shaidawa cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma ina shaida cewa Annabi Muhammad bawanSa ne kuma ManzonSa ne. Sai Allah - mai girma da daukaka - ya cewa wannan mutumin: ka zo wurin ma’aunin ka. Sai mutumin ya ce, yana mai mamaki; Ya Ubangiji! Menene nauyin wannan katin tare da wadannan fayilill din ??. Sai Allah - mai girma da daukaka - ya ce: Wani zalinci ba zai afku akanka ba. Sai ya ce ; sai a dora fayilillikan a ma'aunin, katin ma a daya ma'aunin; sai ma'aunin da fayilillkan suke a ciki su yi sauki, sai ma'aunin da katin yake ciki ya rinjaya, kuma ya yi nauyi, sai Allah Ya gafarta masa.

Koyarwar hadisin: Lallai cewa Allah zai tseratar da wani mutum daga al'um…

Rukunan : FALALOLI · FALALOLIN TAUHIDI · ILIMIN AƘIDA · FALALOLI DA LADUBBA · Imani da Ranar Lahira

بسم الله الرحمن الرحيم Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
بدر Cikakken Wata Rana 16.5 / 29.5
Haske 97%
Wata Sabo a cikin kwana 13
حسبنا الله ونعم الوكيل Allah Ya isa mana, Shi ne mafi kyawun Mai Kiyaye

إِنَّ ٱللَّهَ وَمَلَٰٓئِكَتَهُۥ يُصَلُّونَ عَلَى ٱلنَّبِىِّ ۚ يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ صَلُّوا۟ عَلَيْهِ وَسَلِّمُوا۟ تَسْلِيمًا

Lalle, Allah da malã'ikunSa sunã salati ga Annabi. Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku yi salãti a gare shi, kuma ku yi sallama dõmin amintarwa a gare shi.

Al-Ahzab 33:56

Salati ga Manzon Allah