Yayin da Allah Ya halicci Aljanna da wuta, sai Ya aiki (Malaika) Jibril - aminci ya tabbat…

Musulunci > Ha > Hadith > Ilimin aida > Yayin da Allah Ya halicci Aljanna da wuta, sai Ya aiki (Malaika) Jibril - aminci ya tabbat…

Wanda ya ruwaito hadisin: Abu Dawud da Tirmizi da Nasa'i ne Suka Rawaito shi

Hasan ne

An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26

📖 Karatu minti 2

Rubutun hadisin: Yayin da Allah Ya halicci Aljanna da wuta, sai Ya aiki…

عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه عَنْ رَسُولِ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: «لَمَّا خَلَقَ اللَّهُ الْجَنَّةَ وَالنَّارَ أَرْسَلَ جِبْرِيلَ عَلَيْهِ السَّلَامُ إِلَى الْجَنَّةِ، فَقَالَ: انْظُرْ إِلَيْهَا وَإِلَى مَا أَعْدَدْتُ لِأَهْلِهَا فِيهَا. فَنَظَرَ إِلَيْهَا فَرَجَعَ، فَقَالَ: وَعِزَّتِكَ لَا يَسْمَعُ بِهَا أَحَدٌ إِلَّا دَخَلَهَا. فَأَمَرَ بِهَا فَحُفَّتْ بِالْمَكَارِهِ، فَقَالَ: اذْهَبْ إِلَيْهَا فَانْظُرْ إِلَيْهَا وَإِلَى مَا أَعْدَدْتُ لِأَهْلِهَا فِيهَا. فَنَظَرَ إِلَيْهَا، فَإِذَا هِيَ قَدْ حُفَّتْ بِالْمَكَارِهِ، فَقَالَ: وَعِزَّتِكَ لَقَدْ خَشِيتُ أَنْ لَا يَدْخُلَهَا أَحَدٌ. قَالَ: اذْهَبْ فَانْظُرْ إِلَى النَّارِ وَإِلَى مَا أَعْدَدْتُ لِأَهْلِهَا فِيهَا. فَنَظَرَ إِلَيْهَا فَإِذَا هِيَ يَرْكَبُ بَعْضُهَا بَعْضًا، فَرَجَعَ فَقَالَ: وَعِزَّتِكَ لَا يَدْخُلُهَا أَحَدٌ. فَأَمَرَ بِهَا فَحُفَّتْ بِالشَّهَوَاتِ، فَقَالَ: ارْجِعْ فَانْظُرْ إِلَيْهَا. فَنَظَرَ إِلَيْهَا فَإِذَا هِيَ قَدْ حُفَّتْ بِالشَّهَوَاتِ، فَرَجَعَ وَقَالَ: وَعِزَّتِكَ لَقَدْ خَشِيتُ أَنْ لَا يَنْجُوَ مِنْهَا أَحَدٌ إِلَّا دَخَلَهَا».

Bayanin hadisin: Yayin da Allah Ya halicci Aljanna da wuta, sai Ya aiki…

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa lokacin da Allah Ya halicci Aljanna da wuta, ya cewa (Malaika) Jibril - aminci ya tabbata agare shi -: Ka tafi zuwa ga Aljanna ka duba ta, sai ya tafi ya kallace ta sosai sannan ya dawo, Sai (Malaika) Jibril ya ce: Eh, ya Ubangiji, na rantse da buwayarKa ba wanda zai ji labarin ta da kuma abinda ke cikinta na ni'ima da girmamawa da alkarai sai ya so ya shigeta, kuma ya yi aiki saboda ita. Sannan Allah Ya kewaye Aljanna da abubuwan ki da wahalhalu na aikata umarni da kuma nisantar abubuwan da aka hana; to ya wajaba ga wanda yake son shigarta da ya ketare wadananan abubuwan kin. Sannan Allah - mai girma da daukaka - ya ce: Ya Jibril! ka tafi ka duba Aljanna, bayan ya kewayeta da abubuwan ki, Sai ya tafi ya dubata, sannan ya zo sai ya ce: Eh, ya Ubangiji, na rantse da buwayarKa ina jin tsoro da kada wani ya kasa shigarta saboda wahalhalu da tsananin da suke akan hanyarta. Lokacin da Allah Ya halicci wuta, sai ya ce; Ya Jibri! ka tafi ka kallaceta, sai ya tafi ya kallaceta. Sannan ya zo sai (Malaika) Jibril ya ce: Eh ya Ubangiji, na rantse da buwayarKa babu wani da zai ji labarin azabarta da tashin hankalin cikinta, sai ya ki shigarta ya nisanta daga sabubban shigarta. Sannan Allah - mai girma da daukaka - Ya kewaye wuta, Ya sanya hanya zuwa gareta da sha'awowi da abubuwan jin dadi, sannan Ya ce: Ya Jibril, ka tafi ka yi duba zuwa gareta, Sai (Malaika) Jibril ya tafi sai ya yi duba zuwa gareta, sannan ya dawo sai ya ce: Ya Ubangiji, na rantse da buwayarKa hakika na ji tsoro na ji tausayin kada wani ya kasa tsira daga gareta; saboda abinda ke gefanta na sha'awowi da abubuwan jin dadi.

Koyarwar hadisin: Yayin da Allah Ya halicci Aljanna da wuta, sai Ya aiki…

Rukunan : ABUBUWA MASU TAUSASA ZUKATA DA WA'AZOZI · ILIMIN AƘIDA · SIFFOFIN ALJANNA DA WUTA · FALALOLI DA LADUBBA · Imani da Ranar Lahira

بسم الله الرحمن الرحيم Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
بدر Cikakken Wata Rana 16.6 / 29.5
Haske 96%
Wata Sabo a cikin kwana 13
حسبنا الله ونعم الوكيل Allah Ya isa mana, Shi ne mafi kyawun Mai Kiyaye

إِنَّ ٱللَّهَ وَمَلَٰٓئِكَتَهُۥ يُصَلُّونَ عَلَى ٱلنَّبِىِّ ۚ يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ صَلُّوا۟ عَلَيْهِ وَسَلِّمُوا۟ تَسْلِيمًا

Lalle, Allah da malã'ikunSa sunã salati ga Annabi. Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku yi salãti a gare shi, kuma ku yi sallama dõmin amintarwa a gare shi.

Al-Ahzab 33:56

Salati ga Manzon Allah