Kada ku zauna a kan kaburbura, kada kuma ku yi Sallah kuna kallonsu
Musulunci > Ha > Hadith > Ilimin aida > Kada ku zauna a kan kaburbura, kada kuma ku yi Sallah kuna kallonsu
Wanda ya ruwaito hadisin: Muslim ne ya rawaito shi
Ingantacce ne
An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26
📖 Karatu minti 1
Rubutun hadisin: Kada ku zauna a kan kaburbura, kada kuma ku yi Sallah k…
عن أبي مَرْثَدٍ الغَنَوِيّ رضي الله عنه قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم: «لَا تَجْلِسُوا عَلَى الْقُبُورِ، وَلَا تُصَلُّوا إِلَيْهَا».
Bayanin hadisin: Kada ku zauna a kan kaburbura, kada kuma ku yi Sallah k…
Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya hana zama a kan kaburbura.
Kamar yadda ya hana yin Sallah ana kallon kaburbura, ta yadda kabari zai kasance ta inda alƙiblar mai Sallah take, domin hakan hanya ce ta shirka.
Koyarwar hadisin: Kada ku zauna a kan kaburbura, kada kuma ku yi Sallah k…
- Hana yin sallah a maƙabartu, ko tsakanin kaburbura, ko ana kallon kaburbura, sai dai Sallar janaza kamar yadda hakan ya tabbata a Sunnah.
- Hana yin Sallah ana kallon kaburbura don toshe ƙofar kaiwa ga shirka.
- Musulunci ya hana wuce iyaka a kan kaburbura ya kuma hana wulaƙantasu, ba wuce iyaka, kuma ba wulaƙantawa.
- Alfarmar Musulmi tana nan bayan rasuwarsa, saboda faɗin Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi: Karya ƙashin mamaci kamar karya shi yana raye ne.
Rukunan :
FIƘHU NA IBADA
· SALLAH
· ILIMIN AƘIDA
· FIƘHU DA USULU
· SHARUƊAN SALLAH
· IMANI DA ALLAH MAI GIRMA DA ƊAUKAKA
· Kaɗaita Allah cikin bauta
بسم الله الرحمن الرحيم
Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
أستغفر الله
Ina neman gafara daga Allah