Musulunci > Ha > Hadith > Ilimin aida > Wadannan wasu mutane ne idan bawa na gari ya mutu daga cikinsu, ko kuma mutumin kirki, sai…
Ingantacce neAn sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26
📖 Karatu minti 1عَنْ عَائِشَةَ أُمِّ المؤمنين رضي الله عنها: أَنَّ أُمَّ سَلَمَةَ ذَكَرَتْ لِرَسُولِ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ كَنِيسَةً رَأَتْهَا بِأَرْضِ الْحَبَشَةِ، يُقَالُ لَهَا مَارِيَةُ، فَذَكَرَتْ لَهُ مَا رَأَتْ فِيهَا مِنَ الصُّوَرِ، فَقَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «أُولَئِكَ قَوْمٌ إِذَا مَاتَ فِيهِمُ الْعَبْدُ الصَّالِحُ، أَوِ الرَّجُلُ الصَّالِحُ، بَنَوْا عَلَى قَبْرِهِ مَسْجِدًا، وَصَوَّرُوا فِيهِ تِلْكَ الصُّوَرَ، أُولَئِكَ شِرَارُ الْخَلْقِ عِنْدَ اللهِ».
Uwar muminai Ummu Salama - Allah Ya yarda da ita - ta fadawa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - cewa ta kasance a kasar Habasha ta ga wata coci - ana ce mata Mariya - a cikinta akwai hotuna da kawace- kawace da zane-zane; dan mamaki daga hakan! Sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana dalilan sanya wadannan hotunan; Sai ya ce: Wadannan wadanda kike fada sun kasance idan mutum nagari ya mutu a cikinsu, sai su gina masallaci akan kabarinsa suna sallah a cikinsa, su kuma zazzana wadancan hotunan, ya bayyana cewa mai aikata wancan shi ne mafi sharrin halitta a wurin Allah - Madaukakin sarki -; domin aikata shi yana kaiwa zuwa shirka da Allah - Madaukakin sarki -.
Rukunan : FIƘHU NA IBADA · SALLAH · ILIMIN AƘIDA · FIƘHU DA USULU · IMANI DA ALLAH MAI GIRMA DA ƊAUKAKA · HUKUNCE-HUKUNCEN MASALLATAI · Kaɗaita Allah cikin bauta