Ya bayina lallai ni Na haramta zalunci a kan kaina, kuma na sanyashi abin haramtawa, to, k…

Musulunci > Ha > Hadith > Ilimin aida > Ya bayina lallai ni Na haramta zalunci a kan kaina, kuma na sanyashi abin haramtawa, to, k…

Wanda ya ruwaito hadisin: Muslim ne ya rawaito shi

Ingantacce ne

An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26

📖 Karatu minti 2

Rubutun hadisin: Ya bayina lallai ni Na haramta zalunci a kan kaina, kum…

عن أبي ذر رضي الله عنه: عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ فِيمَا رَوَى عَنِ اللهِ تَبَارَكَ وَتَعَالَى أَنَّهُ قَالَ: «يَا عِبَادِي إِنِّي حَرَّمْتُ الظُّلْمَ عَلَى نَفْسِي، وَجَعَلْتُهُ بَيْنَكُمْ مُحَرَّمًا، فَلَا تَظَالَمُوا، يَا عِبَادِي كُلُّكُمْ ضَالٌّ إِلَّا مَنْ هَدَيْتُهُ، فَاسْتَهْدُونِي أَهْدِكُمْ، يَا عِبَادِي كُلُّكُمْ جَائِعٌ إِلَّا مَنْ أَطْعَمْتُهُ، فَاسْتَطْعِمُونِي أُطْعِمْكُمْ، يَا عِبَادِي كُلُّكُمْ عَارٍ إِلَّا مَنْ كَسَوْتُهُ، فَاسْتَكْسُونِي أَكْسُكُمْ، يَا عِبَادِي إِنَّكُمْ تُخْطِئُونَ بِاللَّيْلِ وَالنَّهَارِ وَأَنَا أَغْفِرُ الذُّنُوبَ جَمِيعًا فَاسْتَغْفِرُونِي أَغْفِرْ لَكُمْ، يَا عِبَادِي إِنَّكُمْ لَنْ تَبْلُغُوا ضَرِّي فَتَضُرُّونِي، وَلَنْ تَبْلُغُوا نَفْعِي فَتَنْفَعُونِي، يَا عِبَادِي لَوْ أَنَّ أَوَّلَكُمْ وَآخِرَكُمْ وَإِنْسَكُمْ وَجِنَّكُمْ كَانُوا عَلَى أَتْقَى قَلْبِ رَجُلٍ وَاحِدٍ مِنْكُمْ مَا زَادَ ذَلِكَ فِي مُلْكِي شَيْئًا، يَا عِبَادِي لَوْ أَنَّ أَوَّلَكُمْ وَآخِرَكُمْ وَإِنْسَكُمْ وَجِنَّكُمْ كَانُوا عَلَى أَفْجَرِ قَلْبِ رَجُلٍ وَاحِدٍ مَا نَقَصَ ذَلِكَ مِنْ مُلْكِي شَيْئًا، يَا عِبَادِي لَوْ أَنَّ أَوَّلَكُمْ وَآخِرَكُمْ وَإِنْسَكُمْ وَجِنَّكُمْ قَامُوا فِي صَعِيدٍ وَاحِدٍ فَسَأَلُونِي فَأَعْطَيْتُ كُلَّ إِنْسَانٍ مَسْأَلَتَهُ مَا نَقَصَ ذَلِكَ مِمَّا عِنْدِي إِلَّا كَمَا يَنْقُصُ الْمِخْيَطُ إِذَا أُدْخِلَ الْبَحْرَ، يَا عِبَادِي إِنَّمَا هِيَ أَعْمَالُكُمْ أُحْصِيهَا لَكُمْ ثُمَّ أُوَفِّيكُمْ إِيَّاهَا، فَمَنْ وَجَدَ خَيْرًا فَلْيَحْمَدِ اللهَ، وَمَنْ وَجَدَ غَيْرَ ذَلِكَ فَلَا يَلُومَنَّ إِلَّا نَفْسَهُ».

Bayanin hadisin: Ya bayina lallai ni Na haramta zalunci a kan kaina, kum…

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana bayyana cewa Allah - tsarki ya tabbatar masa Ya daukaka - Ya faɗi cewa: Ya haramta zalunci a kan kansa, kuma Ya sanya zalunci abin haramtawa a tsakanin bayinsa, kada wani ya zalunci wani. Kuma cewa halitta gaba ɗayansu ɓatattu ne daga hanyar gaskiya sai da shiriyar Allah da dacewarsa, wanda ya roketa zai datar dashi kuma ya shirye shi, kuma cewa halitta mabuƙata ne zuwa ga Allah masu buƙata ne gareshi a dukkanin buƙatunsu, wanda ya roƙi Allah zai biya buƙatarsa Ya kuma isar masa, kuma cewa suna yin zunubai dare da rana, kuma Allah - Maɗaukakin sarki - Yana suturtawa yana yafewa a yayin roƙon bawa gafara, kuma su ba za su iya cutar da Allah ba, ko su amfanar da Shi da komai ba, kuma da ace sun kasance a kan mafi taƙawar zuciyar mutum ɗaya, to, takawarsu ba za ta ƙara komai a mulkin Allah ba, da sun kasance a kan mafi fajircin zuciyar mutum ɗaya, to, fajircinsu ba zai tauye komai daga mulkinsa ba; domin cewa su raunana ne mabuƙata a gurin Allah, masu buƙatuwa zuwa gareshi a kowane hali da zamani da wuri, Shi ne Mawadaci - tsarki ya tabbatar masa -. kuma cewa da ace sun tsaya a bigire ɗaya mutanensu da aljanunsu, na farkonsu da na ƙarshensu suna roƙon Allah sai Ya ba wa kowane ɗaya daga cikinsu abin da ya roƙa, hakan ba zai tauye komai daga abinda ke wurin Allah ba, kamar allura ce da ake shigar da ita kogi sannan a fitar da ita, to, kogin ba zai ragu da komai ba, wannan don cikar wadatarsa tsarki ya tabbatar masa.

Kuma Allah - tsarki ya tabbatar masa Yana kiyaye ayyuakan bayi, Yana tsaresu musu su, sannan Ya cika musu su a ranar alƙiyama, wanda ya samu sakamakon aikinsa alheri, to, ya godewa Allah a bisa dacewa da ya yi ga biyayya gareshi, wanda ya samu sakamakon aikinsa wani abu saɓanin hakan, to, kada ya zargi kowa sai zuciyarsa mai yawan umarni da mummuna wacce ta ja shi zuwa taɓewa.

Koyarwar hadisin: Ya bayina lallai ni Na haramta zalunci a kan kaina, kum…

Rukunan : ILIMIN AƘIDA · IMANI DA ALLAH MAI GIRMA DA ƊAUKAKA · Kaɗaita Allah cikin sunayenSa da siffofinSa

بسم الله الرحمن الرحيم Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
بدر Cikakken Wata Rana 16.5 / 29.5
Haske 97%
Wata Sabo a cikin kwana 13
لا حول ولا قوة إلا بالله Babu wata ƙarfi ko iko sai na Allah

إِنَّ ٱللَّهَ وَمَلَٰٓئِكَتَهُۥ يُصَلُّونَ عَلَى ٱلنَّبِىِّ ۚ يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ صَلُّوا۟ عَلَيْهِ وَسَلِّمُوا۟ تَسْلِيمًا

Lalle, Allah da malã'ikunSa sunã salati ga Annabi. Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku yi salãti a gare shi, kuma ku yi sallama dõmin amintarwa a gare shi.

Al-Ahzab 33:56

Salati ga Manzon Allah