Na rantse da wanda raina yake a hannunsa zaku bi hanyar wadanda ke gabaninku

Musulunci > Ha > Hadith > Ilimin aida > Na rantse da wanda raina yake a hannunsa zaku bi hanyar wadanda ke gabaninku

Wanda ya ruwaito hadisin: Tirmizi da Ahmad sun rawaito shi

Ingantacce ne

An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26

📖 Karatu minti 2

Rubutun hadisin: Na rantse da wanda raina yake a hannunsa zaku bi hanyar…

عَنْ أَبِي وَاقِدٍ اللَّيْثِيِّ رضي الله عنه: أَنَّ رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ لَمَّا خَرَجَ إِلَى حُنَيْنٍ مَرَّ بِشَجَرَةٍ لِلْمُشْرِكِينَ يُقَالُ لَهَا: ذَاتُ أَنْوَاطٍ يُعَلِّقُونَ عَلَيْهَا أَسْلِحَتَهُمْ، فَقَالُوا: يَا رَسُولَ اللهِ، اجْعَلْ لَنَا ذَاتَ أَنْوَاطٍ كَمَا لَهُمْ ذَاتُ أَنْوَاطٍ، فَقَالَ النَّبِيُّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «سُبْحَانَ اللهِ! هَذَا كَمَا قَالَ قَوْمُ مُوسَى {اجْعَلْ لَنَا إِلَهًا كَمَا لَهُمْ آلِهَةٌ} [الأعراف: 138] وَالَّذِي نَفْسِي بِيَدِهِ لَتَرْكَبُنَّ سُنَّةَ مَنْ كَانَ قَبْلَكُمْ».

Bayanin hadisin: Na rantse da wanda raina yake a hannunsa zaku bi hanyar…

Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya fita zuwa Hunain shi: Wani kwari ne tsakanin Makka da Da’if, Ya kasance a tare da shi akwai wasu daga sahabban da ba su dade da shiga Musulunci ba. sai suka wuce wata bishiya ana ce mata: "Ma'abociyar rataya", wato: Ma'abociyar rataye-rataye, mushirikai sun kasance suna girmamata kuma suna rataya makamansu akanta da wasunsu dan neman albarka (sa’a). sai suka nema daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya sanya musu wata bishiyar irinta, za su dinga rataya makamansu akanta, dan neman albarka (sa’a), Dan zatonsu cewa wannan al'amarin ya halatta, sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi tasbihi dan inkarin wannan maganar, da kuma girmama Allah, kuma ya sanar da cewa wannan maganar ta yi kama da maganar mutanen (Annabi) Musa da suka ce da shi: {Ka sanya mana wani ubangiji kamar yadda suke da iyayen giji}, lokacin da suka ga wanda yake bautawa gumaka sai suka nemi ya zama suna da gumaka kamar yadda mushrikai suke da gumaka, kuma cewa wannan bin hanyar hanyarsu ne, sannan tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya bada labarin cewa wannan al'ummar za ta bi hanyar Yahudawa da Nasara kuma za ta aikata irin aikinsu, dan gargadarwa akan hakan.

Koyarwar hadisin: Na rantse da wanda raina yake a hannunsa zaku bi hanyar…

Rukunan : ILIMIN AƘIDA · IMANI DA ALLAH MAI GIRMA DA ƊAUKAKA · Kaɗaita Allah cikin bauta

بسم الله الرحمن الرحيم Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
بدر Cikakken Wata Rana 16.6 / 29.5
Haske 96%
Wata Sabo a cikin kwana 13
اللهم صل على محمد Ya Allah, ka saukar da tsira a kan Muhammad

إِنَّ ٱللَّهَ وَمَلَٰٓئِكَتَهُۥ يُصَلُّونَ عَلَى ٱلنَّبِىِّ ۚ يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ صَلُّوا۟ عَلَيْهِ وَسَلِّمُوا۟ تَسْلِيمًا

Lalle, Allah da malã'ikunSa sunã salati ga Annabi. Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku yi salãti a gare shi, kuma ku yi sallama dõmin amintarwa a gare shi.

Al-Ahzab 33:56

Salati ga Manzon Allah