Yayin da Allah ya suranta Annabi Adam a cikin Al-janna ya barshi lokacin da Allah ya so ya…

Musulunci > Ha > Hadith > Ilimin aida > Yayin da Allah ya suranta Annabi Adam a cikin Al-janna ya barshi lokacin da Allah ya so ya…

Wanda ya ruwaito hadisin: Muslim ne ya rawaito shi

Ingantacce ne

An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26

📖 Karatu minti 1

Rubutun hadisin: Yayin da Allah ya suranta Annabi Adam a cikin Al-janna…

عن أنس بن مالك رضي الله عنه أن رسول الله صلى الله عليه وسلم قال: «لما صوَّرَ اللهُ آدمَ في الجنة تركه ما شاء الله أن يتركه، فجعل إبليسُ يُطيفُ به، ينظر ما هو، فلما رآه أجوفَ عَرف أنه خُلِقَ خَلْقًا لا يَتَمالَك».

Bayanin hadisin: Yayin da Allah ya suranta Annabi Adam a cikin Al-janna…

Yayin da Allah ya halicci nAnnabi Adam a cikin Aljanna kuma ya tsara Surarsa, sai ya barshi wani lokaci bai busa masa rai ba, sai Iblis ya rika kewaye gefensa, yana Kallons; don yasan wane abu ne wannan, yayin da ya ga cikin sa babu komai, sai yasan cewa shi Halitta ce Mai rauni da ba zata iya juriya ba wajen Waswasinsa, ko ya san cewa shi zai iya zuwa da zunubi ta hanyar cikinsa, saboda haka aka zo masa ta hanyar Bishiya, ko kuma ya kasance ya sani cewa yasan Halitta mai ciki rarrauna ce, kuma wasu Mutane sun kasa gane fadinsa: "Cikin Al-janna" tare da cewa abunda ya zo cewa Allah ya halicci Annabi Adam daga bangarorin Kasa, sai ka amsa musu da cewa shi an barshi a haka ne har tsawon lokaci har kirarsa ta zamanto yadda zata iya Karbar Rai, sannan aka dauke shi zuwa Al-janna kuma aka busa Masa rai a cikinta.

Rukunan : ILIMIN AƘIDA · IMANI DA ALLAH MAI GIRMA DA ƊAUKAKA · Kaɗaita Allah cikin sunayenSa da siffofinSa

بسم الله الرحمن الرحيم Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
بدر Cikakken Wata Rana 16.6 / 29.5
Haske 96%
Wata Sabo a cikin kwana 13
الحمد لله Alhamdulillah - Godiya ta tabbata ga Allah

إِنَّ ٱللَّهَ وَمَلَٰٓئِكَتَهُۥ يُصَلُّونَ عَلَى ٱلنَّبِىِّ ۚ يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ صَلُّوا۟ عَلَيْهِ وَسَلِّمُوا۟ تَسْلِيمًا

Lalle, Allah da malã'ikunSa sunã salati ga Annabi. Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku yi salãti a gare shi, kuma ku yi sallama dõmin amintarwa a gare shi.

Al-Ahzab 33:56

Salati ga Manzon Allah