Musulunci > Ha > Hadith > Ilimin aida > Wannan kalmar ta gaske aljani ya fauceta ne, sai ya yi kyarkyararta a kunnen abokin harkar…
Ingantacce neAn sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26
📖 Karatu minti 1عن عائشة رضي الله عنها قالت: سَأَلَ أُنَاسٌ رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ عَنِ الْكُهَّانِ، فَقَالَ لَهُمْ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «لَيْسُوا بِشَيْءٍ» قَالُوا: يَا رَسُولَ اللهِ، فَإِنَّهُمْ يُحَدِّثُونَ أَحْيَانًا بِالشَّيْءِ يَكُونُ حَقًّا، فَقَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «تِلْكَ الْكَلِمَةُ مِنَ الْحَقِّ يَخْطَفُهَا الْجِنِّيُّ فَيَقُرُّهَا فِي أُذُنِ وَلِيِّهِ قَرَّ الدَّجَاجَةِ، فَيَخْلِطُونَ فِيهَا أَكْثَرَ مِنْ مِائَةِ كَذْبَةٍ».
An tambayi Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi dangane da waɗanda suke ba da labarin abin da zai faru nan gaba na gaibu, sai ya ce: Kada ku kula su, kada ku saurari maganarsu, kada ku shiga al’amarinsu.
Sai suka ce: Maganarsu tana daidai da abin da ya faru a wani lokaci, kamar a ce su ba da labarin wani abu na gaibu zai faru a wata kaza a rana kaza, sai kuma ya faru kamar yadda suka faɗa.
Sai Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: Aljanu suna sato abin da suke ji ne na labarun sama, sai su sauko da shi zuwa ga abokan hulɗarsu cikin bokaye, sai su ba su labarin abin da suka ji, sannan sai shi bokan ya ƙara ƙarya ɗari a kan wannan labarin da ya ji daga sama.
Rukunan : ILIMIN AƘIDA · IMANI DA ALLAH MAI GIRMA DA ƊAUKAKA · SUNAYE DA HUKUNCE-HUKUNCE · Kaɗaita Allah cikin bauta · MAS'ALOLIN JAHILIYYA