Dukkanin al'ummata za su shiga aljanna sai wanda ya ƙi

Musulunci > Ha > Hadith > Ilimin aida > Dukkanin al'ummata za su shiga aljanna sai wanda ya ƙi

Wanda ya ruwaito hadisin: Bukhari ne ya rawaito shi

Ingantacce ne

An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26

📖 Karatu minti 1

Rubutun hadisin: Dukkanin al'ummata za su shiga aljanna sai wanda ya ƙi

عن أبي هريرة رضي الله عنه أن رسول الله صلى الله عليه وسلم قال: «كُلُّ أُمَّتِي يَدْخُلُونَ الْجَنَّةَ إِلَّا مَنْ أَبَى»، قَالُوا: يَا رَسُولَ اللهِ، وَمَنْ يَأْبَى؟ قَالَ: «مَنْ أَطَاعَنِي دَخَلَ الْجَنَّةَ، وَمَنْ عَصَانِي فَقَدْ أَبَى».

Bayanin hadisin: Dukkanin al'ummata za su shiga aljanna sai wanda ya ƙi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - yana ba da labarin cewa dukkanin al'ummarsa za su shiga aljanna sai wanda ya ƙi!

Sai sahabbai - Allah Ya yarda da su - suka ce: Wa zai ƙi ya Manzon Allah?!

Sai (manzon Allah) tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi ya amsa musu cewa: wanda ya miƙa wuya ya bi Manzo - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - zai shiga aljanna, amma wanda ya saɓa bai miƙa wuya ga shari'a ba, to, haƙiƙa ya hanu daga shiga aljanna da ayyukansa munana.

Koyarwar hadisin: Dukkanin al'ummata za su shiga aljanna sai wanda ya ƙi

Rukunan : ILIMIN AƘIDA · Imani da Manzanni · ANNABIMMU MUHAMMAD TSIRA DA AMINCIN ALLAH SU TABBATA A GARESHI

بسم الله الرحمن الرحيم Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
بدر Cikakken Wata Rana 16.5 / 29.5
Haske 96%
Wata Sabo a cikin kwana 13
سبحان الله Subhanallah - Tsarkin Allah

إِنَّ ٱللَّهَ وَمَلَٰٓئِكَتَهُۥ يُصَلُّونَ عَلَى ٱلنَّبِىِّ ۚ يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ صَلُّوا۟ عَلَيْهِ وَسَلِّمُوا۟ تَسْلِيمًا

Lalle, Allah da malã'ikunSa sunã salati ga Annabi. Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku yi salãti a gare shi, kuma ku yi sallama dõmin amintarwa a gare shi.

Al-Ahzab 33:56

Salati ga Manzon Allah