Lallai cewa Allah Maigirma da Daukaka ya nade mun kasa, sai da nagano daga bangon gabas zu…

Musulunci > Ha > Hadith > Sira da tarihi > Lallai cewa Allah Maigirma da Daukaka ya nade mun kasa, sai da nagano daga bangon gabas zu…

Wanda ya ruwaito hadisin: Ibnu Majah ne ya Rawaito shi - Abu Daud Ya Rawaito shi - Ahmad ne ya rawaito shi - Muslim ne ya rawaito shi

Ingantacce ne

An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26

📖 Karatu minti 2

Rubutun hadisin: Lallai cewa Allah Maigirma da Daukaka ya nade mun kasa,…

عن ثوبان رضي الله عنه أن رسول الله صلى الله عليه وسلم قال: "إن الله زَوَى لي الأرض، فرأيت مشارقها ومغاربها، وإن أمتي سيبلغ ملكُها ما زُوِيَ لي منها. وأعطيت الكنْزين الأحمر والأبيض. وإني سألت ربي لأمتي أن لا يهلكها بسَنَةٍ بعامةٍ، وأن لا يُسَلِّطَ عليهم عدوا من سوى أنفسهم فيَسْتَبِيحَ بَيْضَتَهُمْ؛ وإن ربي قال: يا محمد، إذا قضيتُ قضاءً فإنه لا يُرَدُّ، وإني أعطيتك لأمتك أن لا أهلكهم بسنة عامة، وأن لا أُسَلِّطَ عليهم عدوا من سوى أنفسهم فيَسْتَبِيحَ بَيْضَتَهُمْ ولو اجتمع عليهم مَنْ بأقطارها، حتى يكون بعضُهم يُهْلِكُ بعضًا ويَسْبِي بعضُهم بعضًا".
ورواه البرقاني في صحيحه، وزاد: "وإنما أخاف على أمتي الأئمةَ المضلين، وإذا وقع عليهم السيف لم يرفع إلى يوم القيامة. ولا تقوم الساعة حتى يلحق حي من أمتي بالمشركين، وحتى تعبد فِئامٌ من أمتي الأوثان. وإنه سيكون في أمتي كذابون ثلاثون؛ كلهم يزعم أنه نبي، وأنا خاتم النبيين لا نبي بعدي. ولا تزال طائفة من أمتي على الحق منصورة لا يضرهم من خذلهم حتى يأتي أمر الله تبارك وتعالى".

Bayanin hadisin: Lallai cewa Allah Maigirma da Daukaka ya nade mun kasa,…

Wannan Hadisi ya kunshi abubuwa kamar haka masu ggirma wadanda suka kunshi Al'amura muhimmai da kuma labarai na gaskiya, kuma wanda Maigaskiya abin gasgatawa ya bada labari, cewa Allah mai girma da daukaka ta tattare masa kasa har saida ya gano abinda Al'umma rsa zata Mallaka tun daga Bangon Duniya na gabas zuwa na yamma, kuma ya bada labari cewa Allah ya bashi Taskoki guda biyu, kuma hakan ya wakana kamar yadda ya bada labarin, kuma ya ce Al'ummarsa zata Mallake Mulkin Kisa da kuma Kaisar da duk abinda suke da shi na zinari da Azurfa da kayan kawa, kuma ya bada labarin cewa ya roki Ubangijinsa kada ya hallaka Al'ummarsa da da fari, ko kuma ya dora Mata abokin gaba daga cikin kafirai wanda zai wanda zai Mamaye garuruwansu kuma ya karar da Jama'arsu, kuma Allah ya amsa masa na farko, kuma ya amsa masa na biyun ma matukar Al'ummarsa ta nisanci sabani da kuma rarrabuwa, da kuma gaba a n tsakaninta, kuma Annabi ya jiyewa Al'ummarsa tsoron Hadarin Batattun Shugabanni da kuma Malamai; domin Mutane da su suke koyi cikin batansu, kuma ya bada labari cewa Fitina zata afku da kuma Yaki to cewa hakan zai ci gaba har zuwa tashin Alkiyamakuma hakika hakan ya faru kamar yadda, to tunda fitinar ta faru kuma ita ce take ci gaba har yanzu, kuma ya bada labarin cewa wasu daga cikin Al'ummarsa zasu koma cikin kafirai can garuruwansu da Addininsu, kuma cewa wasu Jama'u daga cikin Al''umma zasu koma shirka kuma hakan ya faru kamar yadda ya bada labari, don an bautawa Kaburbura da Bishiyoyi da Duwatsu duk da faruwar wadan nan Masifi da hadura, kuma wannan Jama'a ta gaskiya duk da karancintabata cutu da kaidin Abokan gabarta ba da kuma wadanda suka saba mata.

Rukunan : SIRAR ANNABI · ƊABI'U IRIN NA (ANNABI) MUHAMMAD · SIFFOFINSA NA HALITTA · JINƘANSA TSIRA DA AMINCIN ALLAH SU TABBATA A GARESHI · SIRA DA TARIHI

بسم الله الرحمن الرحيم Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
بدر Cikakken Wata Rana 16.5 / 29.5
Haske 97%
Wata Sabo a cikin kwana 13
الحمد لله Alhamdulillah - Godiya ta tabbata ga Allah

إِنَّ ٱللَّهَ وَمَلَٰٓئِكَتَهُۥ يُصَلُّونَ عَلَى ٱلنَّبِىِّ ۚ يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ صَلُّوا۟ عَلَيْهِ وَسَلِّمُوا۟ تَسْلِيمًا

Lalle, Allah da malã'ikunSa sunã salati ga Annabi. Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku yi salãti a gare shi, kuma ku yi sallama dõmin amintarwa a gare shi.

Al-Ahzab 33:56

Salati ga Manzon Allah