Musulunci > Ha > Hadith > Ilimin aida > Lallai Allah - mai girma da daukaka - yana hanaku ku rantse da iyayenku
Ingantacce neAn sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26
📖 Karatu minti 1عَنْ عُمَرَ بْنِ الْخَطَّابِ رضي الله عنه قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «إِنَّ اللهَ عَزَّ وَجَلَّ يَنْهَاكُمْ أَنْ تَحْلِفُوا بِآبَائِكُمْ»، قَالَ عُمَرُ: فَوَاللهِ مَا حَلَفْتُ بِهَا مُنْذُ سَمِعْتُ رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ نَهَى عَنْهَا ذَاكِرًا وَلَا آثِرًا.
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa Allah - Madaukakin sarki - Yana hani daga rantsuwa da iyaye, duk mai nufin yin rantsuwa kada ya rantse da kowa sai da Allah, kada ya rantse da waninsa. Sannan Umar Dan Khaddab - Allah Ya yarda da shi - ya ambaci cewa shi bai sake rantsuwa da su ba tunda ya ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana hani game da hakan, bada gangan ba, ba kuma yana mai cirato rantsuwa da wanin Allah daga waninsa ba.
Rukunan : ILIMIN AƘIDA · IMANI DA ALLAH MAI GIRMA DA ƊAUKAKA · Kaɗaita Allah cikin bauta