Musulunci > Ha > Hadith > Ilimin aida > Duk wanda ya ce: Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, ya kuma kafircewa abin da ake bau…
Ingantacce neAn sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26
📖 Karatu minti 1عن طارق بن أشيم الأشجعي رضي الله عنه قال: سمعت رسول الله صلى الله عليه وسلم يقول: «مَنْ قَالَ: لَا إِلَهَ إِلَّا اللهُ، وَكَفَرَ بِمَا يُعْبَدُ مِنْ دُونِ اللهِ حَرُمَ مَالُهُ وَدَمُهُ، وَحِسَابُهُ عَلَى اللهِ».
Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana bayanin wanda ya faɗa kuma ya shaida da bakinsa: Babu abin bautawa da cancanta sai Allah. Wato babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma ya kafircewa abin da ake bautawa da ba Allah ba, ya barranta da dukkanin addinai ban da Musulunci, to, haƙiƙka dukiyarsa da jininsa sun haramta a kan Musulmai, ba abin da muke da shi sai zahirin aikinsa, ba za a kwace dukiyarsa ba, ba za a zubar da jininsa ba, sai dai idan ya aikata wani laifi, ko ɓarna da za ta tabbatar da hakan a Hukunce Hukuncen Musulunci.
Allah Shi ne Yake jiɓintar hisabinsa ranar Alƙiyama, idan ya yi da gaskiya a ba shi lada, idan kuma munafiki ne a yi masa azaba.
Rukunan : ILIMIN AƘIDA · IMANI DA ALLAH MAI GIRMA DA ƊAUKAKA · Kaɗaita Allah cikin bauta