Wanda ya rantse sai ya ce a cikin rantsuwarsa: Na rantse da Lata da Uzza, to ya ce: Babu a…
Musulunci > Ha > Hadith > Ladubba na sharia > Wanda ya rantse sai ya ce a cikin rantsuwarsa: Na rantse da Lata da Uzza, to ya ce: Babu a…
Wanda ya ruwaito hadisin: Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Ingantacce ne
An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26
📖 Karatu minti 1
Rubutun hadisin: Wanda ya rantse sai ya ce a cikin rantsuwarsa: Na rants…
Bayanin hadisin: Wanda ya rantse sai ya ce a cikin rantsuwarsa: Na rants…
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana gargaɗi akan rantsuwa da wanin Allah; inda mumini ba ya rantsuwa sai da Allah kadai, kuma yana bada labarin cewa wanda ya yi rantsuwa da wanin Allah; kamar wanda ya yi rantsuwa ga misali da: Lata da Uzza - su biyun gumaka ne da ake bauta musu a lokacin Jahiliyya kafin Musulunci - to ya wajaba akansa ya ce yana mai riskar abin da ya fada da kansa: Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, dan kuɓuta daga shirka, da kaffara daga wannan rantsuwar tasa.
Sannan tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya bada labarin cewa wanda ya ce wa abokinsa: Zo mu yi wasan caca, - ita ce mutum ko sama da haka su yi rinjayeyeniya akan wata dukiyar da wani zai ɗauka a tsakaninsu, kuma kowanne daya daga cikinsu ba ya zama haka kodai yaci riba a cikinta ko kuma ya faɗi -; to an so ya yi sadaka da wani abu dan kaffara daga abinda ya yi kira zuwa gare shi.
Koyarwar hadisin: Wanda ya rantse sai ya ce a cikin rantsuwarsa: Na rants…
- Rantsuwa bata kasancewa sai da Allah da sunayenSa da kuma siffofinSa.
- Rantsuwa da wanin Allah - Maɗaukakin sarki - haramun ce, daidai ne rantsuwace da gumaka kamar Lata da Uzza, ko rantsuwa da amana, ko rantsuwa da Annabi ko wanin hakan.
- AlKhaɗɗabi ya ce: Rantsuwa kawai tana kasancewa ne da abin da ake bautawa abin girmamawa, idan ya yi rantsuwa da Lata da makacinsa to haƙiƙa ya yi kama da kafirai, sai aka umarce shi ya riski abinda ya fada da kalmar Tauhidi.
- Babu kaffarar rantsuwa akan wanda ya yi rantsuwa da wanin Allah, kawai ya wajaba akan shi ya koma ga Allah da neman gafara; domin ta wuce ayi mata kaffara sai dai tuba.
- Haramcin caca da dukkan surorinta da yanayinta, itace cacar da Allah - Maɗaukakin sarki - Ya haramta kuma Ya haɗata da giya da gumaka.
- Wajabcin barin saɓo a lokacin aikata shi .
- Wanda ya afka a cikin wani mummunan abu to ya wajaba akansa ya bi shi da kyakkyawa; domin kyawawan ayyuka suna tafiyar da munanan ayyuka.
Rukunan :
LADUBBA NA SHARI'A
· LADUBBAN MAGANA DA SHIRU
· FALALOLI DA LADUBBA
· ABUBUWAN DA AKA HANA FURTAWA DA ILLOLIN HARSHE
بسم الله الرحمن الرحيم
Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
الله أكبر
Allah Shi ne Mafi Girma